logo

HAUSA

Shugaba Xi Jinping ya gana da shugaban kasar Afirka ta Kudu

2022-11-15 20:04:59 CMG Hausa

Da yammacin yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa a tsibirin Bali dake kasar Indonesia.

A yayin ganawar, shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, Sin tana raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Afirka ta Kudu bisa manyan tsare-tsare, kuma tana son su kara imani da juna a fannin siyasa, da sa kaimi ga samun ci gaba kan raya dangantakarsu a dukkan fannoni. Ya ce Sin tana son yin mu’amala da kasar Afirka ta Kudu kan fasahohin tafiyar da harkokin siyasa da kasa, da goyon bayan Afirka ta Kudu wajen neman hanyar zamanintar da kanta bisa nata salo, da kara hadin gwiwa tsakanin shawarar “ziri daya da hanya daya” da shirin sake bunkasa tattalin arziki da farfadowa na kasar Afirka ta Kudu, da zurfafa hadin gwiwarsu a fannonin cinikayya da zuba jari, da makamashi da sauransu, da sa kaimi ga aiwatar da ayyukan da aka cimma daidaito kansu a gun taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, wanda aka yi a kasar ta Afirka ta Kudu, da goyon bayan kamfanonin Sin don su zuba jari a kasar, da kuma fadada fitar da kayayyakin Afirka ta Kudu zuwa kasar Sin.

A nasa bangare, shugaba Ramaphosa ya bayyana cewa, Sin muhimmiyar abokiya ce ta kasar Afirka ta Kudu bisa manyan tsare-tsare, kuma kasarsa za ta ci gaba da goyon bayan ka’idar Sin daya tak a duniya. Kana Afirka ta Kudu tana son koyon fasahohin Sin a fannonin samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da kyautata tsarin makamashi, da shiga ayyukan raya shawarar “ziri daya da hanya daya”, da kuma kara bude kofa ga kamfanonin Sin don sa kaimi gare su, wajen zuba jari da hadin gwiwa a kasar.

A wannan rana kuma, shugaba Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Netherland Mark Rutte, da firaministan kasar Australia Anthony Albanese. (Zainab)