Ana kara habaka hadin-gwiwar Sin da Afirka wajen raya sana’ar noma
2022-11-15 14:21:12 CMG Hausa
Sin kasa ce mai tasowa mafi girma a duniya, kuma Afirka nahiya ce dake cike da kasashe masu tasowa a duniya, kana, zurfafa hadin-gwiwar Sin da Afirka, kyakkyawan fata ne ga al’ummomin bangarorin biyu. Hausawa kan ce, noma tushen arziki. Sana’ar noma ta dade da zama daya daga cikin muhimman fannonin hadin-gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka daban-daban. Tun da aka kafa dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka a shekara ta 2000, wanda aka fi sani da dandalin FOCAC, ya zuwa yanzu, musamman a shekaru 10 da suka shige, bangarorin biyu sun kara habaka hadin-gwiwarsu a fannin aikin gona, musamman a bangarorin da suka shafi kyautata tsari, da zuba jari, da horas da kwararru da makamantansu. Ana iya cewa, kwalliya ta biya kudin sabulu.
A ‘yan shekarun nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya sha sanar da wasu muhimman matakai, a fannin karfafa hadin-gwiwar kasarsa da kasashen Afirka, ciki har da fannin aikin gona. A watan Disambar shekara ta 2015, a wajen taron kolin dandalin FOCAC wanda aka yi a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu, Xi ya ce, kasarsa za ta raba nata dabarun raya sana’ar gona ga kasashen Afirka, da karfafa gwiwar kamfanonin kasar don su kaddamar da ayyukan shuke-shuke, da kiwon dabbobi da sarrafa hatsi a nahiyar Afirka, ta yadda za’a kara samar da guraban ayyukan yi da kudin shiga ga mazauna wurin. A watan Satumbar shekara ta 2018 kuma, a wajen bikin kaddamar da taron kolin dandalin FOCAC da aka gudanar a birnin Beijing na kasar Sin, Xi Jinping ya bayyana cewa, kasarsa za ta goyi bayan nahiyar Afirka wajen cimma burin samun isasshen abinci kafin shekara ta 2030, da hada kai tare da Afirka wajen tsarawa, gami da aiwatar da shirin bunkasa ayyukan noma na zamani da sauransu. Daga baya a watan Nuwambar shekara ta 2021, a wajen bikin kaddamar da taron ministoci karo na 8 na dandalin FOCAC, shugaba Xi ya sanar da cewa, kasarsa za ta taimakawa kasashen Afirka aiwatar da wasu muhimman ayyuka 10 a fannonin da suka shafi rage talauci da sana’ar noma, da tura wasu kwararrun aikin noma 500 zuwa Afirka, har ma da kafa wasu cibiyoyin musanya fasahohin ayyukan noma na zamani, da samar da horo na hadin-gwiwar Sin da Afirka a kasar Sin.
Domin takaita nasarorin da aka samu, da yin hangen nesa ga makomar hadin-gwiwar Sin da Afirka a bangaren aikin noma, kwanan baya, aka shirya wani kasaitaccen biki mai taken “Daren Samun Girbi Tsakanin Sin Da Afirka” a Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda jami’an diflomasiyyar kasashen Afirka dake kasar Sin, da wakilan wasu kungiyoyin kasa da kasa dake Beijing, gami da jami’an ma’aikatun harkokin waje da na aikin noma na kasar suka halarci bikin.
Liu Yuxi, wakili ne na musamman na gwamnatin kasar Sin kan harkokin nahiyar Afirka, ya gabatar da wani muhimmin jawabi a wajen bikin, inda a cewarsa, tun bayan da aka kafa dandalin FOCAC, zuwa yanzu, musamman a shekaru 10 da suka wuce, an kara samun nasarori wajen habaka hadin-gwiwar Sin da Afirka a fannin aikin gona.
Mista Liu ya ce:
“Bana, shekara ce ta farko, da aka aiwatar da nasarorin da aka samu a wajen taron ministoci karo na 8 na dandalin FOCAC. Duk da manyan sauye-sauyen da ake samu a fadin duniya, amma kasar Sin da kasashen Afirka suna marawa juna baya, da kiyaye halaltattun hakkokin kasashe masu tasowa, gami da tabbatar da adalci a duniya. Sin da Afirka suna ci gaba da maida hankali kan karfafa hadin-gwiwa da samar da ci gaba, don aiwatar da muhimman nasarorin da aka samu a wajen taron ministoci karo na 8 na dandalin FOCAC.”
Liu ya kara da cewa, kasar Sin ta dade da kokarin samar da abinci ga duk duniya, da bayar da tata gudummawa a fannin kawar da talauci. Yana mai cewa:
“Kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa kan gaskiya, da nuna sahihanci, da kara hada kai da kasashen Afirka a fannin raya shawarar ‘ziri daya da hanya daya’, da tabbatar da shawarar samar da ci gaba, da tabbatar da tsaro a duniya, ta yadda dandalin FOCAC zai kara amfanar al’ummomin kasashen Afirka.”
Shi ma a nasa bangaren, mataimakin shugaban sashin kula da hadin-gwiwar kasa da kasa na ma’aikatar raya ayyukan gona da yankunan karkara ta kasar Sin, Peng Tingjun, cewa yayi, samar da isasshen abinci, gami da raya yankunan karkara, daya ne daga cikin muhimman fannonin dake jawo hankalin kasar Sin da na kasashen Afirka, wanda ya kamata a ba wa fifiko. Peng ya ce:
“Kasar Sin za ta ci gaba da bude kofar ta ga kasashen waje a fannin aikin gona, da samar da ci gaba mai inganci wajen fadada hadin-gwiwa a fannin aikin gona, da more kimiyya da fasahar aikin gona tare da sauran kasashe, musamman kasashen Afirka, a wani kokari na zurfafa hadin-gwiwar Sin da Afirka a fannin aikin gona, da kara samar da alfanu ga baki dayan al’ummomin bangarorin biyu.”
Bikin ya kuma samu halartar wasu manyan jami’an diflomasiyyar kasashen Afirka dake kasar Sin, wadanda suka taya kasar murnar gudanar da babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar karo na 20, da taya Xi Jinping murnar sake zama babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar, inda a cewar su, kasar Sin ta samu babban ci gaba da manyan nasarori a sabon zamanin da muke ciki, kuma an cimma tudun dafawa wajen karfafa hadin-gwiwar Sin da Afirka a fannin aikin gona. Sun ce, samar da isasshen abinci, da raya manufofi masu dorewa, gami da fadada kirkire-kirkire a fannin fasahohi, muhimman dalilai ne da suka jawo babban ci gaban kasar Sin. Ya dace kasashe masu tasowa, musamman kasashen Afirka, su koyi dabarun kasar Sin daidai bisa hakikanin halin da suke ciki, don tabbatar da ajandar samar da ci gaba mai dorewa kafin shekara ta 2030.
Ambasada Olawale Emmanuel Awe, shi ne mataimakin jakadan tarayyar Najeriya dake kasar Sin, wanda ya zama daya daga cikin baki ‘yan kasashen Afirka da suka halarci bikin, ya yi tsokaci kan hadin-gwiwar Najeriya da China, yana mai cewa:
“Tun bayan da Najeriya ta kulla dangantakar diflomasiyya tare da kasar Sin a shekara ta 1971, ya zuwa yanzu, huldodin kasashen biyu sun samu manyan nasarori, har ma suna ci gaba da bunkasa a halin yanzu. Kasar Sin ta taimaki Najeriya wajen raya sana’ar noma, musamman a fannonin da suka shafi musayar fasahohi da horas da ‘yan Najeriya, domin daidaita matsalar karancin abinci, da samar da isasshen abinci ga Najeriya.”
A wajen bikin dai, akwai wakilan daliban kasashen Afirka daban-daban, wadanda a yanzu haka suke neman karo ilimi a makarantun kasar Sin, musamman a jami’o’in birnin Beijing. Agbo Patience Ndidiamaka, daliba ce ‘yar asalin tarayyar Najeriya, wadda ke karatu a jami’ar koyon ilimin aikin gona ta kasar Sin, ko kuma “China Agricultural University” a Beijing. A cewar ta, aikin noma daya ne daga cikin muhimman sana’o’in dake taimakawa ci gaban Najeriya. Kuma ya dace kasashen Afirka su yi koyi daga kasar Sin a fannin aikin gona, inda ta ce:
“A kasar Sin na ga abubuwa da yawa, da ziyartar yankunan karkara a larduna daban-daban, ciki har da lardin Yunnan, inda na ganewa idanuna abubuwan dake wakana a can. Gwamnatin wurin tana maida matukar hankali wajen raya ayyukan gona. Ina baiwa gwamnatocin kasashen Afirka shawara, da su yi koyi daga yadda kasar Sin take yi wajen raya aikin gona.”
Agbo Patience Ndidiamaka ta ce, a Najeriya wadda ke da dimbin albarkatun man fetur da Allah ya hore mata, wasu mutane ba sa daukar sana’ar noma a matsayin aiki mai muhimmanci, har ma wasu na ganin cewa, sana’a ce ta matalauta. Saboda haka, tana son yin amfani da ilimin da ta koya a kasar Sin wajen gina kasar ta Najeriya, da yin kira ga al’ummar kasar, musamman matasa, da su kara rungumar aikin noma, saboda a cewar malam Bahaushe, “Noma Tushen Arziki”. (Murtala Zhang)