logo

HAUSA

A Dauki Hakikakin Matakai Domin Kyautata Hulda A Tsakanin Sin Da Amurka

2022-11-15 21:03:30 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Amurka Joe Biden sun gana da juna a tsibirin Bali na kasar Indonesia bisa shawarar Amurka jiya da yamma. A yayin ganawarsu ta tsawon awoyi fiye da 3, shugabannin 2 sun yi musayar ra’ayoyi dangane da huldar da ke tsakanin kasashen 2, da manyan al’amuran kasa da kasa da shiyya-shiyya ba tare da rufa-rufa ba, sun kuma samu ra’ayi daya a wasu fannoni, kana sun tabbatar da manufar raya huldar da ke tsakanin Sin da Amurka. Ma iya cewa, an cimma burin tuntubar juna, da kara sanin burikan juna, da shata layin da ba za a ketare ba, da kauracewa ta da rikici, da tabbatar da alkibla da tattaunawa kan hadin gwiwa.

Ainihin dalilin da ya sa huldar da ke tsakanin Sin da Amurka ta yi tsami yanzu haka, shi ne domin Amurka ba ta kallon kasar Sin bisa sanin ya kamata. Ta mayar da kasar Sin abokiyar takara mafi girma, tare da yunkurin mayar da Sin saniyar ware. Abubuwa marasa dacewa da Amurka take yi sun sanya huldar da ke tsakanin Sin da Amurka ta kauce daga hanyar da ta dace. Don haka shugaba Xi Jinping ya jaddada a yayin ganawar cewa, wajibi ne Sin da Amurka su sauke nauyin dake wuyansu, domin moriyar kasa da kasa da jama’ar duniya, su lalubo hanyar da ta dace wajen yin mu’amala da juna a sabon zamani, a kokarin ganin huldar da ke tsakanin kasashen 2 ta koma hanyar da ta dace.

Ganawar da shugabannin Sin da Amurka suka yi a tsibirin Bali ta tabbatar da manufar raya hulda a tsakanin kasashen 2 a wani wa’adi mai zuwa. Kasashen 2 suna bukatar aiwatar da muhimman ra’ayoyi da shugabannin suka cimma, musammam ma Amurka tana bukatar hada kai da Sin, ta yadda za a kara fahimtar yadda babbar kasa take sauke nauyin dake wuyanta ba tare da rufa-rufa ba. (Tasallah Yuan)