logo

HAUSA

Kyautata Alakar Sin Da Amurka Na Iya Shawo Kan Matsalolin Duniya

2022-11-15 18:37:26 CMG Hausa

Yayin da taron koli na kungiyar G20 zai mayar da hankali wajen tattauna muhimman batutuwan da ke ciwa duniya tuwo a kwarya, kamar na tattalin arziki da wadatar abinci da makamashi da batun Ukraine da sauransu, ya samar da wata muhimmiyar dama ta tattaunawar keke da keke, tsakanin shugabannin manyan kasashen duniya biyu, wato Sin da Amurka.

 Karon farko tun bayan hawansa karagar mulkin Amurka, shugaba Joe Biden ya gana ido da ido da takwaransa na kasar Sin Xi Jinping a jiya, gabanin taron.

Hakika, wannan wata dama ce ta warware zare da abawa game da batutuwan dake haifar da tsamin dangantaka tsakanin manyan kasashen biyu.

Amurka ta dade tana takalar kasar Sin da gangan, yayin da a kullum, kasar Sin kan gargadi Amurkar tare da jan hankalinta game da muhimmancin girmama juna da hadin gwiwa a tsakaninsu.

Da alama za a samu saukin abubuwa, duba da yadda shugaban na Amurka ya nanata cewa, matsayar kasarsa ta kiyaye manufar Sin daya tak a duniya ba ta sauya ba, kuma ba ta son gogayya tsakaninsu ta rikide zuwa rikici. Gogayya ko Takara mai tsafta tsakanin manyan kasashen biyu mai, za ta iya zama mai amfanawa al’ummunsu da kuma duniya, muddun Amurka ba ta ci gaba da yin amai tana lashewa ba. Kamata ya yi ta dauki shawarar kasar Sin, wato mutunta juna da girma cikakken ’yanci da moriyar juna, su kasance tushen huldar kasashen biyu. Kana akwai bukatar ’yan siyasar Amurka, su fahimta tare da kiyaye furucin na shugabansu, su dakatar da duk wani yunkurin lalata dangantaka a tsakanin kasashen biyu da neman haddasa rigima.

Kamar yadda shugaba Xi Jinping ya bayyana, a matsayinsu na shugabannin manyan kasashe biyu, ya kamata su lalubo hanyar da ta dace da kyautata dangantakarsu, domin yanayin da take ciki a yanzu, ba ta dace da moriyarsu da ma ta daukacin al’ummar duniya ba.

Ba shakka, kasashen duniya na mayar da hankalinsu ga irin yanayin da Sin da Amurka ke ciki. Kyautata alaka a tsakaninsu za ta iya magance sama da rabin batutuwan da duniya ke fuskanta. Haka kuma, za ta kasance abun koyi ga kasashe masu tasowa. Ya kamata Amurka ta mara baya ga yunkurin Sin na tallafawa kasashe masu rauni da ma wadanda ke tasowa, maimakon ta rika yi mata zagon kasa ko neman bata mata suna. Sin ta yi an gani, kuma tana ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a duniya duk da tarin nauyin al’umma biliyan 1.4 dake wuyanta a cikin gida. Idan har da gaske Amurka na son kyautata dangantakarsu domin duniya baki daya ta amfana, ya kamata ta dakatar da rajinta na bata sunan kasar Sin da yada karairayi, ta rungumi hanyar zaman lafiya da bayar da gudunmawa ga kokarin Sin domin kai wa ga gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil adama.  (Fa’iza Mustapha)