logo

HAUSA

Wang Yi ya yi bayani game da ganawar shugabannin Sin da Amurka

2022-11-15 11:07:28 CMG Hausa

Jiya Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Amurka Joe Biden, a tsibitin Bali na kasar Indonesiya. Bayan ganawar ta su, mamban majalisar gudanarwa, kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi karin bayani ga kafofin watsa labarai game da ganawar shugabannin biyu.

Wang Yi ya ce, ganawar shugabannin biyu na da muhimmiyar ma’ana, domin wannan shi ne karo na farko da shugaban kasar Sin da na Amurka suka yi ganawa fuska ta fuska cikin shekaru 3 da suka gabata, kuma karo na farko da shugabannin biyu suka gana da juna fuska ta fuska, bayan shugaban kasar Amurka Joe Biden ya kama aiki. Kaza lika, wannan shi ne karo na farko, da shugabannin koli na kasar Sin da na Amurka suka yi mu’amala, bayan sun kammala muhimman taruka cikin kasashensu.

Game da batun dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, Wang Yi ya ce, a yayin ganawar shugabannin biyu, an tabbatar da cewa, za a magance tabarbarewar dangantaka a tsakanin kasashen biyu, yayin da ake neman wata hanyar da ta dace ta daidaita dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka. Kuma, za a tattauna cikin hadin gwiwa, domin fidda manufar daidaita dangantaka tsakanin kasashen biyu. Sa’an nan kuma, an fara yunkurin aiwatar da ra’ayin shugabannin biyu, ta yadda za a daidaita dangantakar dake tsakanin kasashen biyu cikin yanayin zaman karko.

Haka kuma, a yayin ganawar tasu, shugabannin biyu sun mai da hankali kan batun lardin Taiwan na kasar Sin. Wang Yi ya ce, kasar Sin na fatan Amurka za ta aiwatar da matakai masu nasaba da hakan, kamar yadda ta bayyana, da kuma bin manufar “kasar Sin kasa daya tak a duniya”, da sanarwar hadin gwiwa guda uku da kasar Sin da Amurka suka kulla, da kaucewa bata yanayin lardin Taiwan.

Dangane da wannan batu, shugaba Biden ya ce, kasar Amurka tana tsayawa tsayin daka kan manufar “kasar Sin kasa daya tak a duniya”, kuma ba ta goyon bayan ballewar yankin Taiwan daga kasar Sin, kana kasar Amurka ba ta da burin hana bunkasuwar kasar Sin ta hanyar rura wutar batun Taiwan.

Dangane da ci gaban da kasashen biyu suka samu a fannin habaka hadin gwiwa bisa fannoni daban daban, Wang Yi ya ce, a yayin ganawar shugabannin biyu, shugaba Xi Jinping ya ce, bai kamata a dakatar da aikin raya dangantaka a tsakanin kasar Sin da kasar Amurka sakamakon bambancinsu ba, kuma ya kamata kasashen biyu su dukufa wajen tsawaita jerin hadin gwiwar dake tsakaninsu.

Bugu da kari, a yayin ganawar tasu, shugaba Xi ya bayyana matsayin kasar Sin kan wasu batutuwan dake janyo hankulan kasar Amurka, da ma sauran kasashen duniya. Shugabannin biyu, sun kuma yi musayar ra’ayoyi kan batutuwan dake shafar kasar Ukraine, da batun nukiliyar zirin Koriya da dai sauransu. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)