logo

HAUSA

Türkiye: An kama mutane 48 da ake tuhumarsu da laifin tayar da bom a titin da ke kusa da filin Taksim

2022-11-15 15:23:19 CMG Hausa

Kafofin yada labaru na kasar Türkiye sun ruwaito cewa, ana bin bahasin fashewar bom a wani titi dake kusa da filin Taksim na birnin Istanbul, birni mafi girma a kasar, inda mutane a kalla shida suka rasu, kuma wasu 81 suka ji rauni. Yawan mutane da aka kama wadanda ake tuhumarsu da laifin tayar da bom din ya kai 48, ciki hadda baki 37. 

Kana kuma an sake bude titin ga al'umma. (Tasallah Yuan)