logo

HAUSA

Xi Jinping ya gana da shugaban Faransa Emmanuel Macron

2022-11-15 11:30:18 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron, a tsibirin Bali da safiyar Talatar nan.

Yayin zantawar su, shugaba Xi ya bayyana cewa, a matsayinsu na muhimman kasashe biyu a duniya, kamata ya yi Sin da Faransa, da kuma Sin da Turai, su tsaya tsayin daka da kafafun su wajen kyautata hadin gwiwa mai budewa, ta yadda dangantakar bangarori biyu za ta gudana lami lafiya bisa turba madaidaiciya.

Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin ta tsaya tsayin daka kan manufar bude kofa ga kasashen waje, tana kuma kokarin ingiza zamanintarwa iri na Sin, wanda zai samar da sabbin damammaki ga kasashen duniya, ciki har da Faransa.

Xi ya kara da cewa, bangaren Sin yana son nuna goyon baya ga aikin Indonesiya tare da bangaren Faransa, domin cimma nasarar kammala taron kolin G20 a tsibirin Bali, da karfafa mu’ammala da hadin gwiwa a fannonin tinkarar matsalar sauyin yanayi, da kare nau’o’in halittu mabambanta, da cimma manufar gudanar da harkokin kasa da kasa tsakanin bangarori daban daban, da tinkarar kalubalolin da duk duniya ke fuskanta, kamar samar da isasshen abinci da makamashi mai inganci, tare kuma da samu ci gaba mai dorewa.

Macron ya kuma taya shugaba Xi Jinping murnar sake zama babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin, da nasarar kammala babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta Sin karo na 20. Ya ce yana jinjinawa tsarin ci gaban zamani na Sin. Kaza lika bangaren Faransa ya nuna goyon bayan diplomasiyya mai zaman kan ta, tare da adawa da yaki tsakanin sassa daban daban. (Safiyah Ma)