logo

HAUSA

Li Keqiang ya gana da babban sakataren MDD

2022-11-14 10:57:16 CMG Hausa


Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya gana da babban sakataren MDD António Guterres, a birnin Phnom Penh na kasar Kambodiya da yammacin jiya Lahadi. Yayin ganawar tasu, Li Keqiang ya bayyana cewa, MDD hukuma ce mai muhimmanci dake kiyaye ra’ayin bangarori daban daban. Kuma bangaren Sin ya yabi sabbin nasarorin da hukumomin MDD suka cimma, karkashin jagorancin babban sakatare Guterres. Kaza lika ya yi fatan MDD za ta ci gaba da mu’ammala da hadin gwiwa, da nuna goyon bayan bunkasuwar tattalin arziki cikin lumana, da tinkarar sauyin yanayi ga kasashe masu tasowa.

Guterres ya bayyana cewa, hadin gwiwar Sin da MDD babban ginshiki ne na cudanyar bangarori daban daban. Ya ce MDD ta yabi gudummawar da Sin ta bayar a fannin kiyaye cudanyar bangarori daban daban, da inganta ajandar tinkarar sauyin yanayi da ci gaba mai dorewa. Kuma ana fatan MDD za ta karfafa hadin gwiwa tare da bangaren Sin.

A jiya ne kuma, Firaministran Li Keqiang ya kammala ziyarar aikinsa, ya kuma dauki jirgin sama ya baro babban birnin Phnom Penh na Kambodiya ya dawo nan Beijing. (Safiyah Ma)