logo

HAUSA

Shugabannin Sin Da Amurka Sun Gana Yau A Bali

2022-11-14 20:00:33 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na Amurka Joe Biden, sun gana a yau Litinin, gabanin taron kolin kungiyar G20 da zai gudana a tsibirin Bali na kasar Indonesia.

A cewar Xi Jinping, ya kamata kasashen biyu su waiwayi tarihi, kuma ya zama alkiblar da za su bi a nan gaba. Ya ce yanayin da ake ciki yanzu game da dangantakar Sin da Amurka, bai dace da moriyar kasashen biyu da al’ummominsu ba, haka kuma bai dace da fatan al’ummar kasa da kasa ba. Kuma a matsayinsu na shugabannin manyan kasashe biyu, ya kamata su lalubo hanyar da ta dace da kyautata dangantakarsu.

Ya kara da cewa, al’ummun kasa da kasa na sa ran ganin Sin da Amurka sun tafiyar da dangantakarsu ta hanyar da ta dace, yana mai cewa, ganawarsu ta yau, za ta ja hankalin duniya baki daya. A don haka, ya kamata su hada hannu da sauran kasashe wajen kara fatan wanzuwar zaman lafiya a duniya, da kwarin gwiwa kan kwanciyar hankalin duniya da ingiza ci gaba na bai daya.

Bugu da kari, shugaban na Sin ya ce yana sa ran hada hannu da shugaba Biden domin mayar da dangantakar kasashen biyu bisa turbar da ta dace da samun ingantaccen ci gaba domin moriyar kasashen biyu da ma daukacin duniya.

“Hakkinmu ne nuna cewa, Sin da Amurka za mu iya hakuri da bambance-bambancen dake tsakaninmu da kaucewa rikidar takara zuwa rikici, da lalubo hanyoyin hadin gwiwa kan muhimman batutuwan duniya. Da ni da Xi, muna sa ran ci gaba da tattaunawa bisa gaskiya ba tare da rufa-rufa ba kamar yadda aka yi a baya.” a cewar shugaba Biden. (Fa’iza Mustapha)