logo

HAUSA

Shugaba Xi Jinping ya amsa wasikar ma’aikatan masana’antar kera jiragen sama

2022-11-13 17:21:27 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya amsa wasikar tawagar matasa masu koyon halayyen Luo Yang, ta kamfanin Shenfei na masana’antar kera jiragen saman kasar Sin, inda ya bayyana goyon bayansa gare su, wajen bayar da gudummawa kan raya kasa a fannin masana’antar kera jiragen sama.

Cikin amsar da ya bayar a jiya, Shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, yana fatan membobin tawagar za su sa kaimi ga raya kimiyya da fasahar kera jiragen sama, da samar da gudummawa wajen samun ci gaba a masana’antar, da kuma raya kasa ta zamani bisa tsarin gurgurzu a dukkan fannoni da samun farfadowar al’ummar Sinawa.

A ranar 26 ga watan Nuwamban shekarar 2012, shugaba Xi Jinping ya yi jawabi game da rasuwar Luo Yang, babban direktan kamfanin Shenfei na masana’antar kera jiragen saman kasar Sin, kuma babban mai ba da umurni a wurin binciken jiragen saman yaki samfurin J-15, inda ya bukaci ma’aikata su yi koyi da halayyen Luo Yang. Tun daga shekarar 2013, yawan tawagar matasa masu koyon halayyen Luo Yang ta kamfanin da suka yi aiki tare da daidaita matsaloli bisa halayyen Luo Yang, ya kai dubu 370. A kwanakin baya, wakilin tawagar ya mika wasika ga shugaba Xi, inda ya yi bayani game da abubuwan da membobin tawagar suka samu yayin da suke aiki da karatu a kamfanin, tare da nuna imaninsu na bayar da gudummawarsu ga kasar Sin. (Zainab)