logo

HAUSA

Australia: kila kara cin ‘ya’yan itatuwa zai rage barazanar kamuwa da ciwon sukari mai nau’in 2

2022-11-13 17:30:23 CMG Hausa

 

Jami’ar Edith Cowan ta kasar Australia ta kaddamar da rahoton nazari a kwanan baya cewa, akwai wata alaka a tsakanin kara cin danyun ‘ya’yan itatuwa a ko wace rana, da kuma raguwar barazanar kamuwa da ciwon sukari mai nau’in 2.

Jami’ar ECU ta ce, ta yi amfani da bayanai dangane da ‘yan Australia dubu 7 da dari 6 da 75, wadanda cibiyar nazarin ciwon zuciya da ciwon sukari ta Australia ta tattara bayanan domin gudanar da bincike. Ta tantance yawan ‘ya’yan itatuwa, yawan ruwan ‘ya’yan itatuwa da kuma yawan masu kamuwa da ciwon sukari bayan shekaru 5. Sakamakon ya nuna cewa, idan mutane su kan ci ‘ya’yan itatuwa a kalla giram dari 3 a ko wace rana, to, bayan shekaru 5, barazanar da suka fuskanta wajen kamuwa da ciwon sukari mai nau’in 2 zata ragu da kaso 36.

Ko da yake binciken ya tabbatar da kasancewar wata alaka a tsakanin kara cin danyun ‘ya’yan itatuwa a ko wace rana, da kuma raguwar barazanar kamuwa da ciwon sukar mai nau’in 2. Amma bai tabbatar da cewa, ko dalilin da ya sa raguwar barazanar, shi ne kara cin ‘ya’yan itatuwa a ko wace rana ba.

Yanzu ciwon sukari mai nau’in 2 yana kara addabar al’ummomin kasa da kasa. An kimanta cewa, mutane kimanin miliyan 450 suna fama da ciwon a duk fadin duniya, yayin da wasu miliyan 370 suke fuskantar karuwar barazanar kamuwa da ciwon.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, idan wasu sun kara cin ‘ya’yan itatuwa, su kan rage yawan sukari da ke jininsu amma ba sa fitar da sinadarin insulin mara yawa a jiki, hakan yana da muhimmanci ga lafiya. Saboda idan ana fitar da sinadarin insulin da yawa a jiki don rage yawan sukari da ke jini, to, za a lahanta jijiyoyin jini, da kuma kara barazanar kamuwa da ciwon sukari, ciwon zuciya da ciwon hawan jini. Duk da haka ba a san yadda kara cin ‘ya’yan itatuwa ya ke ba da tasiri kan fitar da sinadarin insulin a jiki ba tukuna.

Bayan da haka kuma, kar a sha ruwan ‘ya’yan itatuwa a maimakon cin su don yin rigakafin kamuwa da ciwon sukari. Dangane da haka, madam Zhang Chuji, likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta ce, kila saboda akwai sukari da yawa a cikin ruwan ‘ya’yan itatuwa, amma sinadarin fiber ba su da yawa. Danyun ‘ya’yan itatuwa sun hada da sinadarin bitamin, ma’adinai, abubuwa masu gina jiki na tsirrai da sinadarin dake taimaka ga narkas da abinci a jikin mutum, wadanda suke taka muhimmiyar rawa wajen rage barazanar kamuwa da ciwon sukari mai nau’in 2. (Tasallah Yuan)