logo

HAUSA

Wang Yi ya halarci bikin bude cibiyar sa kaimi ga samun ci gaban duniya

2022-11-13 17:15:16 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya halarci bikin bude cibiyar sa kaimi ga samun ci gaban duniya a jiya, inda ya bayyana cewa, a watan Yunin bana, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar a gun taron tattaunawa tsakanin manyan shugabanni kan ci gaban duniya cewa, Sin za ta kafa cibiyar sa kaimi ga samun ci gaban duniya. A jiya ne kuma aka kafa cibiyar da bude ta a hukunce, lamarin da ta zama sabon matakin da Sin ta dauka don aiwatar da kiran samun ci gaban duniya da zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa.

Wang Yi ya bayyana cewa, tun bayan da shugaba Xi Jinping ya gabatar da kiran samun ci gaban duniya, Sin take kokarin sa kaimi ga hadin kan kasa da kasa, da aiwatar da muhimman matakai 32, da kuma samun wasu nasarori.

Wang Yi ya jaddada cewa, Sin za ta kara zuba jari ga hadin gwiwar samun ci gaba a duniya, da kafawa da amfani da cibiyar yadda ya kamata, don mai da ta matsayin muhimmin dandalin sa kaimi ga aiwatar da kiran samun ci gaba a duniya, da bayar da gudummawa wajen cimma burin ajandar samun ci gaba mai dorewa ta shekarar 2030 ta MDD cikin lokaci. (Zainab)