logo

HAUSA

Wang Yi Ya Halarci Taron Kasa Da Kasa Kan Fasahar Tagwaita Irin Shinkafa Da Wadatar Abinci A Duniya

2022-11-13 17:02:07 CMG Hausa

Mamban majalisar gudunarwar kasar Sin kuma Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi ya halarci taron kasa da kasa kan fasahar tagwaita irin shinkafa da wadatar abinci a duniya, wanda aka yi jiya a birnin Beijing.

A cewar Wang Yi, babban taron wakilan JKS karo na 20 da aka kammala a baya-bayan nan, ya bayyana cewa, kasar Sin za ta bayar da sabbin gudunmuwa ga ci gaban bil Adama ta hanyar zamanantar da kanta, inda sabon ci gaban da kasar za ta samu, za ta samar da sabbin damarmaki ga duniya.

Ya kara da cewa, fasahar tagwaita irin shinkafa, wani ci gaba ne a tarihin kimiyya da fasahar aikin gona na kasar Sin, wadda ba taimakawa Sin wajen samun wadatar abinci kadai ta yi ba, har ma da bayar da gagarumar gudunmuwa wajen warware matsalar karancin abinci a duniya.

Ya ci gaba da cewa, Sin ta dauki wadatar abinci a matsayin daya daga cikin bangarorin da take ba muhimmanci a shirin raya duniya, yana mai cewa a shirye Sin take ta hada hannu da sauran kasashe da hukumomin kasa da kasa, domin bayar da karin gudunmuwa ga tabbatar da wadatar abinci a duniya da cimma muradun ci gaba masu dorewa na shekarar 2030. (Fa’iza Mustapha)