logo

HAUSA

Li Keqiang Ya Halarci Taron Kolin Gabashin Asiya Karo Na 17

2022-11-13 21:21:07 CMG Hausa

Da safiyar yau Lahadi, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya halarci taron kolin gabashin Asiya karo na 17 a birnin Phnom Penh, hedkwartar kasar Cambodia, inda shugabanni ko wakilai na kasashe mambobin kungiyar ASEAN da kasashen Amurka, Japan, Koriya ta Kudu, Australia, New Zealand, Indiya da Rasha suka halarta.

A yayin taron, Li Keqiang ya ce, ya kamata kasashen da ke yankin su mutunta juna da zurfafa hadin gwiwarsu domin samun moriyar juna, da shawo kan barazana tare. Ya kuma gabatar da shawarwari guda 3, da suka hada da, na farko, a tsaya kan tattaunawa bisa manyan tsare-tsare da yin mu’amala da juna yadda ya kamata. Ya ce wajibi ne a kara azama, don  kasashen dake yankin su yi shawarwari da tattaunawa, domin amincewa da juna, da daidaita sabani, da kaucewa katse hulda da kiyayya da juna. Na biyu, a tsaya kan yin hadin gwiwa don samun moriyar juna, da tinkarar barazana cikin hadin gwiwa. Ya ce wajibi ne a aiwatar da yarjejeniyar RCEP yadda ya kamata, a kuma tabbatar da daidaiton tsarin masana'antu da samar da kayayyaki da wadatar makamashi da abinci, a kokarin tunkarar sauyin yanayi da matsalolin muhallin halittu tare. Na uku, a tsaya kan sanya kungiyar ASEAN a gaban kome, da kafa tsarin yanki da ya kunshi dukkan sassa. Kana wajibi ne a tabbatar da matsayin kungiyar ta ASEAN. Yana mai cewa, Kasar Sin na goyon bayan kiyaye hadin kan kungiyar. (Tasallah Yuan)