logo

HAUSA

Taron COP27 da hukumar FAO sun kaddamar da shirin taimakawa al’ummomi masu rauni

2022-11-13 16:37:53 CMG Hausa

 

Kasar Masar dake shugabantar taron sauyin yanayi na COP27 da hukumar samar da abinci da raya aikin gona ta MDD (FAO), sun kaddamar da wani shirin raya aikin gona da samar da abinci domin taimakawa al’ummomi mafiya rauni.

Cikin wata sanarwa da aka fitar a jiya, shugabancin taron na COP27 na bangarorin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD, ya ce shirin wanda aka yi wa lakabi da Sauyi mai Dorewa a Bangaren Samar da Abinci da Aikin Gona wato FAST, zai sauya tsare-tsaren aikin gona da na samar da abinci, ta yadda zai samar da nasarori 3 da suka shafi jama’a da yanayi da kuma halittu.

Shugabancin na COP27, ya ce abubuwan da shirin na FAST zai mayar da hankali kansu su ne, samar da kudi da ilimi da fasahohi da kuma manufofin tallafi da tattaunawa.

A cewar shugaban taron na COP27, kuma ministan harkokin wajen Masar, Sameh Shoukry, ta hanyar shirin, za a hada kan kasashen duniya domin su samar da hanyar samun kudade domin kara juriyar sauyin yanayi da gaggauta aiwatar da sauyin da ake bukata a tsare-tsaren aikin gona da samar da abinci. (Fa’iza Mustapha)