logo

HAUSA

Babban jami’in Africa CDC ya jinjinawa kasar Sin bisa hadin gwiwar ta a fannin sarrafa rigakafin COVID-19 a Afirka

2022-11-12 16:59:18 CMG Hausa

Mukaddashin daraktan cibiyar kandagarki da yaki da annobar COVID-19 ta Afirka, ko Africa CDC Ahmed Ogwell Ouma, ya jinjinawa kasar Sin, bisa shiga hadin gwiwar sarrafa alluran rigakafin cutar COVID-19 da ta yi tare da wasu kasashen Afirka.

Mr. Ouma, ya ce hadin gwiwar Sin da kasashe irin su Masar, da Algeria, da Morocco, ya samar da karin dama ta sarrafa rigakafin COVID-19 a cikin nahiyar, musamman a gabar da aka samu yawaitar bazuwar cutar a tsakiyar shekarar 2021 da ta gabata.

Jami’in ya kara da cewa, hadin gwiwar sassan ya baiwa Afirka damar sarrafa rigakafi a cikin nahiyar, matakin da ya rage bukatar safarar sa daga wajen nahiyar. Kaza lika, ya jinjinawa Sin bisa yadda ta rika samarwa Afirka rigakafin kyauta, tun lokacin da aka fara yiwa al’umma alluran.

Mr. Ouma, wanda ya yi wannan tsokaci a gefen bikin kaddamar da shirin kare rayuka, da walwalar al’ummar kudancin Afirka, wanda Afirka CDC da hadin gwiwar gidauniyar Mastercard suka shirya, ya ce an kaddamar da shirin ne domin hade sassan kasashen kudancin Afirka 10, da nufin karfafa musu gwiwar cimma nasarar yiwa al’ummun su rigakafi.

Daga nan sai ya bayyana shirin da ake yi, na kaddamar da makamancin shirin a karin sassan nahiyar 4, ta yadda za a kai ga yiwa kusan kaso 70 bisa dari na al’ummun Afirka, wadanda suka cancanci karbar rigakafin su kimanin biliyan 1.3 alluran, nan da karshen shekarar nan ta 2022.  (Saminu Alhassan)