logo

HAUSA

Li Keqiang: Kasar Sin tana son yin amfani da ci gaban da ta samu don zurfafa hadin gwiwa da rukunin 10+3

2022-11-12 21:29:17 CMG Hausa

Yau Asabar 12 ga wata, yayin da firaministan kasar Sin Li Keqiang ya halarci taron shugabannin kasashen Asiya da Sin, da Japan, da Koriya ta kudu karo na 25 a birnin Phnom Penh na kasar Kambodiya, ya jaddada cewa, kofar kasar Sin za ta kara budewa ga kasashen waje. Kasar Sin tana son kawo sabbin damammaki ga dukkan kasashen duniya ta hanyar ci gaban da ta samu, da kuma zuba sabon kuzari ga zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen ASEAN 10 da kasashen 3 wato Sin, Japan da Koriya ta kudu.

Shugabanni mahalarta taron sun bayyana cewa, kamata ya yi dukkan bangarorin su hada kai, da zurfafa hadin gwiwa a fannoni daban daban, da sa kaimi ga dunkulewar shiyyar, da tinkarar kalubalen duniya tare, da inganta hadin gwiwa da rukunin sassa 10+3, domin kara samun sakamako mai kyau. (Mai fassara: Bilkisu Xin)