logo

HAUSA

Shugaban Najeriya: Afirka na da hakkin neman 'diyyar yanayi' daga kasashen yamma

2022-11-12 17:01:36 CMG Hausa

Shafin yanar gizo na "Washington Post" na Amurka, ya buga wani sharhi mai taken "Kaucewa yin magana game da sauyin yanayi da Afirka " wanda shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi a ranar 9 ga watan Nuwamba.

Sharhin ya yi nuni da cewa, ana yawan samun yawaitar ambaliyar ruwa a kasar sa, amma bai kai wanda aka fuskanta a baya-bayan nan ba. A bana jihohi 34 daga cikin 36 na Najeriya ne lamarin ya shafa, sannan sama da mutane miliyan 1.4 sun rasa matsugunansu.

Buhari ya fada a cikin sharhin cewa, da yawa daga cikin takwarorinsa sun ji takaicin munafunci, da rashin daukar nauyin da kasashen yamma ke yi. Gwamnatocin kasashen yammacin duniya sun sha kasa cika alkawuran da suka dauka, na samar da dala biliyan 100 a duk shekara, a matsayin tallafin shawo kan tasirin sauyin yanayi, don taimakawa kasashe masu tasowa wajen daidaita kalubalen. Yayin da ajandar COP27 ke nuni da bukatuwar diyya ga asara, da lalacewar al’amura sakamakon sauyin yanayin, amma kasashen yamma sun yi shiru a kan wannan bukata.

Afirka ita ce nahiyar da ta fi kusa da kawo karshen matsalar fitar da iskar Carbon. Tana da hakkin sanya albarkatu a kasashen dake cikin ta a tsarin makamashinta. Kuma ba Afirka ce ke jawo matsalar ba, amma ita ke biyan farashin hakan. Don haka makalar ta ce taron na bana, ya kamata ya zama mafarin dukkan shawarwari. (Mai fassara: Bilkisu)