logo

HAUSA

‘Yan wasan harbin bindiga na Sin a gasar 2022 sun ciri tuta

2022-11-11 15:54:00 CRI

‘Yan tawagar wasan harbin bindiga daga kasar Sin, da suka halarci gasar kasa da kasa ta 2022 wadda hukumar ISSF ke shiryawa, sun lashe lambobin yabo masu tarin yawa a birnin Alkahiran Masar.

Yayin gasar da ta kammala a ranar 27 ga watan nan, ‘yan wasan kasar Sin sun lashe lambobin zinari 27, da azurfa 16 da tagulla 15, inda suka kasance tawaga mafi samun lambobin yabo jimilla 58, sai kuma tawagar kungiyar kasar Indiya wadda ke da jimillar lambobi 34, ciki har da zinari 12. Gasar ta bana ta hallara sama da maharba 1,000 daga sama da kasashe da yankuna 80 na duniya.

Kaza lika ‘yan tawagar sun lashe gurabe 8 na shiga gasar Olympic, cikin gurabe 32 da hukumar ISSF ke tanada, ake kuma rabawa daidai, wato takwas-takwas tsakanin rukunonin wasannin da za a fafata a cikin su, a matsayin share fagen shiga gasar Olympic ta birnin Paris da za a yi a shekarar 2024.

Da wannan sakamako, Sin ta zama kasa mafi guraben fafatawa a gasar birnin Paris rukunin maharba, bayan raba sauran guraben gasar harbin karamar bindiga, da na doguwar bindiga ga kasashen nahiyar Turai da masu shiga gasar ta duniya.

Da yake karin haske kan hakan, daraktan hukumar wasan harbin bindiga da kwari da baka na Sin Liang Chun, ya ce "Mun cimma aniyar mu a gasar nan ta kasa da kasa, kuma sakamakon da muka samu ya ingiza kwarin gwiwar mu, da kwazon mu a matsayin tawaga. Mun yi nasara duk da sauye sauye da ISSF ta gudanar a ka’idojin wasan, bayan gasar Olympic ta birnin Tokyo, wanda hakan ya kara matsin lambar nuna kwarewa ga ‘yan wasa kafin su cimma nasara.

Cikin dukkanin gasannin, maharban kananan bindigogi na Sin sun zamo kan gaba wajen karbar lambobin yabo, yayin da aka daga tutar kasar Sin sama sosai. Sun yi nasarar lashe lambobin zinari 4 cikin 10 da aka fafata a kan su, a yayin gasar da ta gudana a zauren wasan harbi dake sabon birnin Olympic dake Masar, kuma sun yi nasara sama da sauran daukacin tawagogin da suka shiga gasar”.

Kari kan hakan, ‘yan wasan harbin na Sin sun nuna kwarewa matuka a babban gasar. Cikin manyan ‘yan wasa 24, 13 an haife su ne bayan shekara ta 2000, kuma duk da haka wasun su sun lashe manyan lambobin yabo. Ga misali, Huang Yuting mai shekaru 16 kacal, ta lashe lambar azurfa a gasar harbi ajin mata daga nisan mita 10, kana ta lashe lambar zinari a gasar hadakar ‘yan wasa.

A ajin masu kananan shekaru, Du Linshu ya lashe lambobin zinari 5, da azurfa 2, yayin da abokin wasan sa Pang Yuqian ya lashe lambobin zinari 4, wanda hakan ya sanya ‘yan tawagar Sin lashe sama da rabin lambobin yabo na gasar.

Game da hakan, mataimakin daraktan hukumar lura da wasan harbin bindiga da kwari da baka na Sin Wang Lian, ya ce kyakkyawan shiri, da atisaye mai tsanani da ‘yan wasan Sin suka samu ne ya ba su damar lashe gasar ta ISSF.

Ya ce "Mun fara shirin shiga wannan gasa ne tun watan Nuwambar 2021, jim kadan bayan gasar Olympic ta birnin Tokyo. Tun daga nan ne kuma, ‘yan wasan mu ke kara mayar da hankali sosai ga samun horo har tsawon shekara guda".

Ko shakka babu, kwazon ‘yan wasan tawagar Sin ya burge ‘yan kallo, inda wasun su suka rika son daukar hotuna tare da su, da ma sauran mashirya da masu karbar bakuncin gasar.

Da yake tsokaci game da kwazon ‘yan wasan kasar Sin, yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, shugaban hukumar lura da wasan harbin bindiga na kasar Masar ko ESF Hazem Hosny, ya ce "Tawagar ‘yan wasan Sin ta lashe lambobin yabo masu yawa, sai kuma ‘yan wasan Indiya dake biye da su. Hakan wata manuniya ce ga ci gaban fannin wasanni na Sin, wanda ya kara bayyana a fili, yayin wannan gasa ta kasa da kasa. Na yi imanin cewa, yawan lambobin yabo da suka lashe a wannan karo, sakamako ne na aiki tukuru da suka kwashe tsawon lokaci suna yi".

A nasa bangare kuwa, jagoran gasar ta hukumar ISSF Uwe Fuchs, cewa ya yi bai yi mamaki ba, ganin yadda Sin ta zamo zakarar gwajin dafi a wannan lokaci. Ya ce "Duk da cewa ba a ga ‘yan wasan Sin a gasanni masu yawa cikin shekaru 2 da suka gabata ba sakamakon cutar COVID-19, amma ana hasashen ‘yan wasan harbi na Sin za su kasance cikin shiri mai kyau, tare da lashe manyan lambobin yabo a gasanni masu zuwa, ciki har da gasar Olympic, da gasannin kasa da kasa dana lashe kofin duniya".

Sai dai kuma duk da haka, darakta Liang na ganin akwai damar kara inganta kokarin tawagar domin tunkarar gasanni na gaba. Musamman a gasannin harbi masu zangon mita 25 da 50, inda ‘yan wasan mu ba su da cikakkiyar kwarewa, kamar sauran zakarun duniya.

Liu Yukun da Lu Zhiming, sun kammala ajin maza na harbin doguwar bindiga daga nisan mita 50 a matsayi na 5 da 6 daga wurare 3, da na nisan mita 25 a ajin harbi da gajerun bindigogi, matakin da ya bawa Sin din damar samun gurbin shiga gasar Olympic, ko da yake ba za a kwatanta hakan da lashe lambar zinari da azurfa da tawagar kasar ta yi ba a gasar Olympics ta birnin Tokyo.

Zhao Yuqing, shi ne manajan ‘yan wasan harbi da kananan bindigogi na kasar Sin, ya kuma bayyana cewa, akwai ‘yan matsalolin da ya dace nan gaba a warware su a fannin samar da horo, ciki har da kwazon ‘yan wasa na kai tsaye, bayan kammalar wannan gasa ta kasa da kasa. Zhao ya kara da cewa, "Ba wata hanya mai sauki ta kaiwa ga nasara. Hanya daya ita ce ta aiki tukuru, tare da bin dabarun kimiyya".

A nasa bangare, mataimakin darakta Wang, ya gargadi ‘yan wasan da su ci gaba da kara kwazon yin atisaye a kullum, ta yadda za su samu gurbi a gasar birnin Paris ta shekarar 2024.

Wang ya ce "Duk wanda ya kai matsayin kwarewa 100 bisa 100 zai samu gurbi a tawagar Sin ta zuwa gasar birnin Paris. Akwai gurbin a yanzu, amma yana hannun kwamitin shirya gasar Olympic na Sin. Dole sai sun yi aiki tukuru, sun yi takara da sauran takwarorin su ta cikakkun tsare-tsaren fitar da gwani. ‘Yan wasa 2 mafiya kwarewa a duk rukunoni ne za su samu zarafin fafatawa a gasar birnin Paris".