logo

HAUSA

Li Keqiang ya gana da fira ministan Kambodia Houn Sen

2022-11-10 13:42:10 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Keqiang wanda yake ziyara kasar Kambodia, ya gana da takwaransa na Kambodia Houn Sen a birnin Phnom Penh a jiya Laraba.

Li Keqiang ya bayyana cewa, bangaren Sin ya dade da daukar duk kasashen duniya a matsayin daidai suke, da goyon bayan bangaren Kambodia ya nemi ci gaba ta hanyar da ta dace da yanayin kasar, da kuma ta taka muhimmiyar rawa a dandalin yankuna da na duniya. Ya ce  Sin tana son hada hannu da manyan shugabannin Kambodia, da goyon bayan juna a kan abubuwan dake shafar moriyarsu da ma abubuwan dake jan hankalinsu, ta yadda za su inganta ci gaban dangantakar abota tsakanin Sin da Kambodian, da kawo alheri ga al’ummar kasashen biyu.

A nasa bangare, Houn Sen ya bayyana cewa, Kambodia da Sin, abokai ne na kwarai. Kuma bangaren Kambodian ya tsaya tsayin daka kan manufar kasar Sin daya tak, da goyon baya ga gina makoma ta bai daya ta Kambodia da Sin. Haka kuma, yana so ya karfafa mu’ammala da hadin gwiwa da Sin, a fannonin cinikayya da zuba jari da noma da manyan ababen more rayuwa da harkokin bil’adam da sauransu. Ya ce kasashen biyu za su hada kai karkashin tsarin bangarori daban daban, ta yadda za su inganta dangantakar abota dake tsakaninsu. (Safiyah Ma)