logo

HAUSA

Shugaba Macron ya sanar da janyewar dakarun Faransa daga yankin Sahel

2022-11-10 13:53:00 CMG HAUSA

 

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sanar da kawo karshen ayyukan rundunar Barkhane ta kasar, a yankin Sahel na nahiyar Afrika a hukumance.

Shugaba Macron, wanda ya bayar da sanarwar jiya a Toulon dake gabashin Faransa, ya ce kasar ba ta da niyyar girke dakarun ba tare da kayyade lokaci ba.

Sai dai, ya kara da cewa, taimkon soji daga Faransa zuwa ga kasashen Afrika a yankin Sahel, zai ci gaba amma ta wata sabuwar siga.

Tun cikin shekarar 2014, Faransa ta girke dakaru 5,100 a kasashe 5 na yankin Sahel, wadanda suka hada da Burkina Faso da Chadi da Mali da Mauritania da kuma Niger, karkashin shiri mai taken Barkhane. Manufar shirin ita ce, taimakawa kasashen 5, tabbatar da ikon kan yankunansu da kare yankin daga zama mafakar kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi.

Faransa za ta tattauna da abokan huldarta na Afrika, kan yadda taimakonta na ayyukan soji za su kasance, da kuma sansanonin tawagarta dake yankin Sahel da yammacin Afrika.

A watan Fabrerun bana ne, Macron ya sanar da cewa, janyewar dakarun Faransa daga Mali, zai dauki watanni 4 zuwa 6. Kuma akwai sojojin kasar kimanin 2500 zuwa 3000 a kasar ta Mali.

Ya kuma nanata muhimmiyar rawa da Faransa da Turai suka taka wajen yaki da ta’addanci a nahiyar Afrika. Yana mai cewa, Faransa za ta ci gaba da yaki a kasashen dake makwabtaka da yankin Sahel, kamar na gabar tekun Guinea da Niger. (Fa’iza Mustapha)