logo

HAUSA

An Yabawa Wasu Manyan Nasarori 15 Da Sin Ta Samu A Fannin Fasahohin Intanet

2022-11-10 14:21:59 CMG Hausa

An yabawa wasu manyan nasarori 15 da Sin ta samu a fannin kimiyya da fasahar intanet, wadanda kuma suka kasance ja gaba a duniya.

Tsarin sadarwa tsakanin na’urori na “IPv6” da aikin samar da na’urorin da harkokin sadarwa na kamfanin China Unicom da kuma manhajar sarrafa na’urori ta OpenEuler da kamfanin Huawei ya samar, na daga cikin abubuwan da suka samu yabo daga wani kwamiti da ya hada masana harkokin intanet 40, da suka fito daga ciki da wajen kasar Sin.

Taron, wani bangare ne na babban taron duniya kan intanet, dake gudana a Wuzhen, na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin. Tun daga watan Mayu ya samu manhajoji sama da 257 daga kasashe da yankunan duniya da suka hada da Sin da Amurka da Rasha da Birtaniya da Sweden.

Wadannan manhajoji, dake kan gaba a bangarorin intanet, sun hada da tsarin sadarwa na 5G da 6G da tsarin IPv6 da tsaron intanet da kananan na’urorin Chip masu matukar inganci, da hidimomin intanet na masana’antu da kere-kere na’urori kwaikwayon tunanin dan Adam da sauransu. (Fa’iza)