logo

HAUSA

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD na yaki da rikice-rikice a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

2022-11-10 10:16:41 CMG HAUSA

 

MDD ta ce jami’an shirinta na wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, na taimakawa hukumomin kasar wajen kandargarki da rage aukuwar rikice-rikice a matakan yankuna.

Kakakin MDD Stephanie Tremblay, ta ce tawagar shirin da aka fi sani da MINUSCA, na kuma taimakawa wajen shirya zama na biyu a bana, na kotun daukaka kara ta Bangui game da laifuffukan da aka aikata. 

A cewar MINUSCA, ana gudanar da shirye-shiryen mataki na gaba, dangane da rage rikice-rikice a yankuna, inda za a ba jama’a, ciki har da matasa, damar kaucewa shiga ayyukan rikici ta hanyar koyon sana’o’in hannu da sauran hanyoyin samun kudin shiga da ajiye makamai bisa radin kansu.

Kakakin ta kara da cewa, tawagar ta MDD na gudanar da sintiri domin kare al’umma da tsaron yankuna masu hadarin fadawa rikici, inda suka yi sintiri kusan sau 1,700 a cikin makon da ya gabata, ciki har da na hadin gwiwa tsakaninsu da dakarun gwamnatin kasar. (Fa’iza Mustapha)