logo

HAUSA

Sin ta kaddamar da cibiyar farko ta nazarin matakan hada-hadar cinikayyar fasahohi domin kasashen Afirka

2022-11-10 21:08:01 CMG Hausa

A jiya Laraba ne kasar Sin ta kaddamar da cibiyar farko, ta nazarin matakan hada-hadar cinikayyar fasahohi domin kasashen nahiyar Afirka, a birnin Changsha fadar mulkin lardin Hunan na kasar.

Babban nauyin da aka dorawa cibiyar shi ne tattara bayanai, da ba da shawarwari, da ingiza sha’anin tabbatar da ingancin hajoji.

Kaza lika cibiyar na da tawagar kwararru mai kunshe da mutane 139, da suka hada da masana a fannin cinikayya da harkokin tattalin arzikin Sin da Afirka, da fannin hada hadar kudade da biyan haraji, da gwajin ingancin hajoji, da fannin injiniyan manyan na’urori, da fannin samar da kayayyakin gudanar da sufurin layin dogo, da albarkatun gona.   (Saminu Alhassan)