logo

HAUSA

Halartar manyan kamfanonin kasa da kasa a fannin Chips bikin CIIE ta nuna aniyarsu ta rungumar kasuwar kasar Sin

2022-11-10 19:38:56 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya yi bayani kan halartar manyan kamfanonin kasa da kasa da dama, a fannin sassan na’urorin laturoni na Chips, wajen bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin wato CIIE a takaice, inda ya nuna cewa, a yayin da ake fama da tabarbarewar tattalin arzikin duniya, da karuwar ra’ayin ba da kariyar da ake samu, wadannan kamfanonin sun shiga baje kolin, wanda hakan ya nuna aniyarsu ta bayyana kwarin gwiwa game da kasar Sin, da rungumar kasuwar kasar.

Kakakin ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa a yau Alhamis 10 ga wata.

A cewar rahotanni, 'yan kwanaki da suka gabata, kamfanonin Intel, da AMD, da Qualcomm, da ASML, da sauran manyan kamfanonin kasa da kasa a fannin samar da sassan na’urorin laturoni na Chips, sun shiga baje kolin CIIE karo na biyar. Jaridar "Financial Times" ta Biritaniya, da sauran wasu kafafen yada labarai sun yi sharhin cewa, takunkumin da Amurka ta kakaba wa kasar Sin a fannin shigar da sassan na’urorin laturoni na Chips, bai raunana kwarin gwiwar da kamfanonin na duniya ke da shi kan kasar Sin ba.

Kakakin ya ba da amsa a yayin da yake mayar da martani ga tambayar da aka yi masa, cewa wannan ya tabbatar da cewa, bunkasuwar kasar Sin mai inganci, da fadada bude kofa ga kasashen waje da kasar ke yi, sun dace da yanayin ci gaba na yanzu. (Mai fassara: Bilkisu Xin)