Manufar bude kofar kasar Sin na amfanawa ci gaban duniya baki daya
2022-11-09 10:15:39 CMG Hausa
Yanzu haka ana gudanar da bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin karo na biyar (CIIE) a birnin Shanghai na kasar Sin, bikin da aka bude a ranar 5 har zuwa ranar 10 ga watan Nuwanban wannan shekara.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana a jawabin da ya gabatar ta kafar bidiyo, yayin kaddamar da bikin cewa, kasar Sin za ta tsaya kan manufarta ta bude kofa ga kasashen ketare, da tsarin dunkulewar tattalin arzikin duniya waje guda, da kokarin mai da ci gaban kasar damar raya tattalin arzikin duniya.
A matsayinsa na bikin baje kolin kasa da kasa na farko a duniya, mai taken shigo da kayayyaki, bikin na CIIE ya kasance wani muhimmin dandali na saye da sayarwa na kasa da kasa, da inganta zuba jari da musaya tsakanin al’ummomi da na al’adu, da hadin gwiwar dake shafar kowa da kowa tun lokacin da aka fara gudanar da shi a shekarar 2018.
Alkaluma na nuna cewa, yayin bukukuwan CIIE guda 4 da aka gudanar a baya, yawan darajar kwangilolin da aka kulla ta kai dalar Amurka biliyan 272.3.
Taken baje kolin na bana dake zama karo na biyar, shi ne kara bude kofa ga kasashen waje, kana shi ne muhimmin bikin baje hajoji da kasar Sin ta gudanar, tun bayan kammalar taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20 a kwanakin baya, kuma bikin CIIE na bana ya ja hankalin dukkanin sassa masu ruwa da tsaki.
Kamar yadda ta sha bayyanawa, kasar Sin za ta ingiza burin dukkanin kasashen duniya na cin gajiya daga damammakin babbar kasuwar kasar, da moriyar dake tattare da kara bude kofar kasar, da zurfafa hadin gwiwar sassan kasa da kasa. Don haka, manufar kasar Sin ta bude kofa, ba kasar kadai za ta amfana ba, har ma da ci gaban ragowar kasashen duniya. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)