logo

HAUSA

An kaddamar da sabon shirin kasuwar Carbon na Afirka a taron COP27

2022-11-09 12:32:04 CMG Hausa

An kaddamar da wani sabon shirin fadada shigar da nahiyar Afirka, cikin kasuwannin Carbon na kashin kai, a yayin taro na 27 na sassan da suka sanya hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD (COP27), da ya gudana jiya Talata a wurin shakatawa na Sharm El-Sheikh dake kasar Masar.

Wata sanarwa da shirin na ACMI karkashin jagorancin wani kwamiti mai mutane 13 da ya kunshi shugabannin kasashen Afirka, da shugabannin gudanarwa, da masana harkokin lamuni a fannin Carbon ya fitar, ya bayyana cewa, an kaddamar da shirin ne da nufin taimakawa bunkasa samar da lamuni da ya shafi iskar Carbon, da ayyukan yi, da kare nau’o’in halittu a Afirka.

Shirin ya kuma sanar da wani gagarumin buri ga nahiyar, na kaiwa ga samar da lamunin Carbon miliyan 300 a kowa ce shekara nan da shekarar 2030.

Wannan mataki zai samar da kudaden shiga da suka kai dalar Amurka biliyan 6 da tallafawa ayyukan yi miliyan 30. A cewar sanarwar, ya zuwa shekarar 2050, shirin na ACMI yana fatan samun lamunin Carbon biliyan 1.5 a duk shekara a Afirka, inda ake fatan samun fiye da dalar Amurka biliyan 120, da taimakawa sama da guraben ayyukan yi miliyan 110.

Kasashen Afirka da dama, wadanda suka hada da Kenya, da Malawi, da Gabon, da Najeriya da kuma kasar Togo, sun yi musayar ra’ayoyi kan yadda za su hada kai da ACMI, don bunkasa samar da lamunin Carbon, ta hanyar shirye-shiryen farfado da kasuwar Carbon na radin kai. (Ibrahim)