logo

HAUSA

Sin ta jima da rungumar manufofin dakile sauyin yanayi

2022-11-09 21:07:41 CMG Hausa

A jiya Talata 8 ga watan nan ne, kasashen da suka jagoranci tarukan masu ruwa da tsaki kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD karo na 26 da 27, sun mikawa tawagar kwararru damar tsara rahoton hadin gwiwa, wanda zai kunshi kira da a samar da jarin da yawan sa zai kai dalar Amurka triiliya 2, domin tallafawa kasashe masu tasowa, a kokarin su na dakilewa, da shawo kan mummunan tasirin sauyin yanayi.

Game da hakan, yayin taron manema labarai na Larabar nan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce matakin da ake bi na shawo kan kalubalen sauyin yanayin duniya, na fuskantar manyan matsaloli. Kuma kasashe masu tasowa su ne suka fi dandana kudar su sakamakon sauyin yanayin.

Jami’in ya kara da cewa, Sin na goyon bayan taron wajen tsara manufofi da suka dace, dangane da takaita asara, da tabarbarewar al’amura da ake fuskanta a kasashe masu tasowa, kuma Sin na kira ga kasashe masu sukuni, da su dauki nauyin da ke bisa wuyansu bisa tarihi, kuma a matakin kasa da kasa na magance sauyin yanayi. Zhao Lijian, ya ce tabbas Sin za ta taimakawa kasashe masu tasowa, a fannin inganta kwarewar su ta tunkarar sauyin yanayi.

Daga nan sai jami’in ya jaddada matsayar kasar Sin, ta ci gaba da yayata manufofin dakile sauyin yanayi. Ya ce Sin ta aiwatar da dabaru daban daban a matakin kasa, domin tabbatar da magance kalubalen sauyin yanayi, da nacewa hanyar fifita kare muhallin halittu, da samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, inda ta cimma manyan nasarori a fannin. (Saminu Alhassan)