logo

HAUSA

AU ta yi kira da a dauki managarta matakan sa kaimi ga ci gaban masana’antun Afirka

2022-11-09 14:49:56 CMG HAUSA

 

Kwamishina mai kula da harkokin raya tattalain arziki, cinikayya, yawon shakatawa, masana’antu da ma’adinai na kungiyar tarayyar Afirka (AU) Albert Muchanga, ya yi kira da a dauki managartan matakai, domin sa kaimi ga dunkulewa da dorewar ci gaban masana’antun Afirka.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar, a yayin taron hadin gwiwa na ministocin kasashen Afirka dake kula da masana’antu, da raya tattalin arziki, da aka gudanar a Niamey, babbar birnin Jamhuryar Nijar.

Muchanga ya bayyana cewa, “ya dace a samar da rayuwa da kara kaimi ga ci gaban masana’antun Afirka, ta hanyar aiwatar da ayyukan yau da kullum dake haifar da kyakkyawan sakamako a fannin kirkire-kirkire, da yin takara, da samar da kayayyaki, da ayyukan yi, da sauransu, da kuma uwa uba, inganta rayuwar talakawa.

Ya kuma jaddada bukatar gina cibiyoyi da aiwatar da manufofin da suka dace, wadanda za su ba da damar gudanar da harkokin kasuwanci, da kafa kamfanoni masu zaman kansu, da kara daidaita manufofin da suka shafi masana’antu da suka wajaba, ta yadda za a kai ga aiwatar da shirye-shiryen raya masana’antu da ayyukan da suka dace ta hanyar sanya ido, da tantance sakamako. (Ibrahim Yaya)