logo

HAUSA

An bude bikin nune-nunen jiragen sama na Sin karo na 14

2022-11-09 15:00:13 CMG Hausa


An bude bikin baje kolin jiragen sama da harkokin sararin samaniya na duniya na Sin karo na 14 ne a birnin Zhuhai dake lardin Guangdong a ranar jiya Talata.

Bikin na bana, ya ja hankalin kamfanonin cikin gida da na waje fiye da 740 daga kasashe da yankuna guda 43, inda suka halarci bikin ta yanar gizo ko a zahiri. Fadin yankin baje koli dake cikin daki ya kai muraba’in mita dubu 100, da jiragen sama da aka nuna fiye da 110, wato filin baje kolin ya kara fadada. Sannan kasashe kamar Amurka da Faransa da Jamus da Italiya da Saudi Arabia da sauransu sun baje sabbin nasarori a fannin sararin samaniya a runfunansu.

Kamfanin kula da masana’antun sararin samaniya na Sin, AVIC a takaice, ya halarci bikin tare da ayyuka da fasahohin zamani na sararin samaniya fiye da 200 da ya nazarta da kuma kirkiro da kansa. A ciki akwai guda 55 da suka shiga bikin a karo na farko. An kuma baje kolin wasu nau’ikan jiragen sama na yaki iri iri da ake kiransu jiragen sama na “zamani na 20”.

Kamfanin Kimiyya da Fasahohin Sararin Samaniya na Sin, wato kamfanin CASC, ya baje rokar Long March 5B, da sabon nau’in rokar dake jigilar yan sama jannati, da babbar rokar dakon kayayyaki masu nauyi da sauran sabbin rokokin dakon na’urori.

Tun bayan da aka kaddamar da bikin a karo na farko a shekarar 1996, nune-nunen harkokin sararin samaniya na Sin ya zama dandali mai muhimmanci na nuna fasahohi da kayayyaki na zamani na Sin da kasashen ketare a fannin sararin samaniya. A sa’i daya kuma ya zama dandalin duniya dake sa kaimi ga hadin gwiwar cinikayya a fannin fasahohi da kayayyaki na sararin samaniya. (Safiyah Ma)