logo

HAUSA

Hukumomin agaji sun yi kira ga kasashen duniya da su dauki matakan gaggawa don kawo karshen matsalar yunwa a yankin kahon Afirka

2022-11-09 12:33:44 CMG Hausa

Hukumomin bayar da agaji na duniya, sun yi kira ga kasashen duniya, da su gaggauta hada kai domin kawo karshen matsalar yunwa a yankin kahon Afirka.

Hukumomin MDD gami da kungiyoyi masu zaman kansu, sun yi kashedin cewa, an samu karuwar matsalar karancin abinci mai gina jiki a cikin shirye-shiryen kula da abinci mai gina jiki a fadin yankin.

Wata sanarwar hadin gwiwa, da hukumomin suka fitar a yammacin ranar Litinin, a birnin Nairobin Kenya ta bayyana cewa, mutane da dama sun rasa abubuwansu na rayuwa, da hanyoyin da za su iya magance wannan bala’i, sannan kuma sun dogara baki daya kan taimako don biyan bukatunsu na yau da kullum, matakin da zai iya kalubalantar farfadowar fari.

A cewar sanarwar, an shiga wani lokaci na fuskantar fari karo na biyar a jere, sakamakon rashin ruwan sama tsakanin watannin Oktoba da Disamba, da zaton da ake na ci gaba da samun kasa da matsakaici na yanayi damina a watannin Maris zuwa Mayun shekarar 2023.

An kuma yi nuni da cewa, duk da karuwar bukata, shirye-shirye na yaki da fari na kasashen Habasha da Kenya da Somaliya, suna samun kaso 50 cikin 100 ne kadai na kudaden da suke bukata, matakin da ya yi matukar takaita karfin hukumomin jin kai na kai agaji.(Ibrahim)