logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya taya murnar bude taron yanar gizo na duniya

2022-11-09 13:56:56 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika da sakon taya murnar bude taron kolin Internet na duniya na shekarar 2022 dake gudana a garin Wuzhen, a yau Laraba.

Cikin sakonsa, shugaban ya ce ci gaban fasahar na’urori masu kwakwalwa wadda ake kira Digital Technology a Turance, sun haifar da sauye-sauye a fannin kimiya da fasaha har ma da masana’antu, kuma tasirinsa ya shafi bangarorin tattalin arziki, da zaman al’umma, da yadda mutane suke aiki, da rayuwa, gami da kula da al’umma. Wannan yanayi, a cewar shugaban, na samar da damammaki da kuma kalubaloli. Don haka, idan har kwalliya ta kara biyan kudin sabulu, ya kamata kasashe daban daban su kara musayar ra’ayi, da zurfafa hadin kansu, baya ga yin kokari tare don samar da tsarin yanar gizo mai adalci, da tsaro, inda ake aiwatar da tunani na bude kofa, da tabbatar da moriyar kowa.

An bude taron koli na Wuzhen ne a yau Laraba, a garin Wuzhen na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin, bisa taken “Hada hannu don kafa al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya a bangaren yanar gizo ta Internet”. (Bello Wang)