logo

HAUSA

Kasar Sin ta kasance ta farko wajen yawaitar mutane masu hazaka a duniya

2022-11-09 16:43:39 CMG Hausa

Yayin da ake gudanar da bikin baje kolin kayayyakin da aka shigo da su kasar Sin na kasa da kasa karo na 5, cibiyar CCG ta gudanar da “dandalin tattaunawa kan yadda mutane masu hazaka suke kai komo da kuma samun ci gaba a duniya”, sannan an fitar da wani rahoto mai alaka na shekarar 2022. 

Rahoton ya nuna cewa, daga cikin manyan kasashe 10 dake kan gaba a fannin takarar mutane masu hazaka a duniya, kasashen Turai da Amurka da na Asiya sun yi kankankan, yayin da cibiyar dake kula da taruwar mutane masu hazaka tana yaduwa daga Turai da Amurka zuwa yankunan Asiya. Daga cikinsu yawan mutane masu hazaka dake nan kasar Sin ya kasance a kan gaba. (Safiyah Ma)