logo

HAUSA

Kamfanin Sin ya haskaka kauyen Lauteye na jihar Kanon Nijeriya

2022-11-08 19:02:50 CMG Hausa

Hasken lantarki, muhimmin bangare ne na ababen more rayuwar dan Adam, musammam a wannan zamani da muke ciki da komai ke da alaka da hasken lantarki. Tsayayyen wutar lantarki ko akasinsa, wani mizani ne na auna ci gaban wuri. Don haka, samun wutar lantarki daga makamashi mai tsafta, wani karin tagomashi ne ga rayuwar bil adama da muhalli.

Na yi wannan shimfida ne bisa la’akari da gagarumar gudunmawar da kamfanin PowerChina ya bayar a baya-bayan nan, inda ya gwangwaje kauyen Lauteye na yankin karamar hukumar Bunkure ta jihar Kano dake arewa maso yammacin Nijeriya, da na’urori 500 na samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana.

Samun wannan labari, ya yi matukar faranta min rai, ganin yadda wani mutumin yankin mai shekaru sama da 40, ya ce kauyen nasu bai taba samun hasken lantarki ba.

Hakika wannan yunkuri na kamfanin kasar Sin zai taimakawa al’ummar kauyen, ta hanyoyi daban-daban. Misali, za a samu ingantuwar tsaro, harkokin kasuwanci za su bunkasa, dalibai za su kara samun damar bitar karatunsu, al’umma za su samu damar more fasahohin zamani, kana za su daina kashe kudin sayen gawayi ko kalanzir ko kyandir da sauransu, haka kuma, ina da yakinin ya bude wa kauyen wani sabon babi na ci gaba.

Yunkurin wani bangare ne na shirin kamfanoni 100 a kauyuka 1,000, wanda kungiyar ’yan kasuwar kasar Sin a Afrika ta kirkiro, da nufin tattara kamfanoni kasar Sin 100, domin su aiwatar da ayyuka 1,000 da  al’ummomin nahiyar za su ci gajiyarsu.

Baya ga taimakawa wajen bunkasa tattalin arzikin nahiyar da samar da guraben ayyukan yi da gudanar da ayyukan agaji, kamfanonin kasar Sin suna kokarin tallafawa al’ummomin kauyuka da ba kowa ne zai tuna da su ba. Shi ya sa a kullum na kan ce, kasar tana da hangen nesa da sanin ya kamata, domin na tabbata, mutanen kauyen da ma jihar Kano, har da kasarmu ba za su manta da irin taimakon da Sin ba. (Fa’iza Mustapha)