logo

HAUSA

Kamfanonin kasar Sin sun gina layin dogo da ya haura tsawon kilomita 10,000 a sassan nahiyar Afirka

2022-11-08 20:22:22 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce karkashin dandalin bunkasa hadin gwiwar Sin da nahiyar Afirka, kamfanonin kasar Sin sun gina layin dogo da tsayin sa ya zarce kilomita 10,000, da kusan kilomita 100,000 na titunan mota, da kusan gadoji 1000, da kusan tashoshin ruwa 100, da tarin asibitoci da makarantu a sassan nahiyar Afirka.

Zhao Lijian ya bayyana hakan ne, yayin taron manema labarai na yau Talata, lokacin da yake amsa tambayar da aka yi masa dangane da sabuwar gadar Wami da aka bude a baya bayan nan a kasar Tanzania, wadda wani kamfanin kasar Sin ya gina. Zhao ya kara da cewa, har kullum karancin manyan ababen more rayuwa na zamewa kasashen Afirka “Kadangaren bakin tulu” ta fuskar ci gaba.

Daga nan sai ya jaddada aniyar kasar Sin, na ci gaba da rike gaskiya da amana, da kare hakikanin yanayi na adalci da cimma moriyar juna, tare da aiwatar da matakan bunkasa hadin gwiwa da kasashen Afirka a fannoni daban daban. Kaza lika Sin za ta dage waje kare moriyar ta da ta al’ummun Afirka, kana za ta shigar da sabon kuzari wajen gina al’ummar duniya mai makomar bai daya tsakanin ta da kasashen Afirka a wannan sabon zamani.   (Saminu Alhassan)