logo

HAUSA

Sirrin wani manomi da ke noman yawan shinkafa a Hubei

2022-11-08 11:15:39 CMG Hausa

Zhang Bin, manomi ne da ke noma mafi yawan shinkafar gundumar Jiangling a lardin Hubei da ke yankin tsakiyar kasar Sin. A lokacin zafi na bana, an dauki kwanaki fiye da 60 ana fama da tsananin zafi a wurin, lamarin da ya kawo babbar illa ga shinkafar da yake nomawa. Mahukuntan wurin sun taimaka wa Zhang Bin da matarsa wajen yaki da fari, a karshe dai sun yi girbin shinkafa mai albarka. Kana kuma sun bi shawarar gwamnatin kasar, sun ci gaba da shuka abubuwan da a kan sarrafa don samun man girki a gonakin da suka girbe shinkafa. Yin shuke-shuke ba tare da tsayawa ba a gonakinsa, ya kara samar wa Zhang Bin da iyalinsa kudin shiga mai yawa. Yanzu iyalin Zhang Bin ya zama abun misali a wurin, wanda yake jagorantar mazauna wurin jin dadin zamansu. (Tasallah Yuan)