logo

HAUSA

'Yan kasuwan Afirka ta Kudu na fatan kara fitar da amfanin gonarsu zuwa kasar Sin

2022-11-08 14:49:49 CMG Hausa

A ‘yan shekarun nan, a kasuwannin kasar Sin, ana kara ganin tufa wato apple a turance, wadanda aka shigo da su daga kasashe daban-daban, ciki har da Afirka ta Kudu. Alkaluman babbar hukumar kwastam ta kasar Sin sun shaida cewa, Afirka ta Kudu ta zama babbar kasa ta biyu, wadda ke fitar da tufa zuwa kasuwannin kasar Sin a shekara ta 2021. ‘Yan kasuwan dake cinikin tufa na Afirka ta Kudu suna da yakini game da makomar kasuwannin kasar Sin, kana suna sa ran kara fitar da amfanin gonarsu masu inganci zuwa kasuwannin kasar Sin.

Jihar Western Cape, muhimmin yanki ne dake samar da tufa a kasar Afirka ta Kudu, inda yake samar da sama da rabin tufan da ake samarwa a fadin kasar. Yankin noman tufa a wannan waje, daya ne daga cikin yankunan noman tufa mafi kusa da layin da ya raba duniyar mu daga yamma zuwa gabas, kuma tufar wannan yanki mai dumi, na da kyan-gani da inganci gami da dandano mai dadi. Tufa mai zaki da dandano mai dadi daga Afirka ta Kudu, yana samun karbuwa daga mutanen kasar Sin, al’amarin dake taimakawa sosai wajen inganta cinikin ‘ya’yan itatuwa tsakanin kasashen biyu. Dan kasuwan dake fitar da ‘ya’yan itatuwan Afirka ta Kudu zuwa kasashen waje, Vincent Keesenberg ya bayyana cewa, tufar Afirka ta Kudu na da inganci, wanda ke iya biyan bukatun kasuwannin kasar Sin, yana mai cewa:

“Afirka ta Kudu tana kara fitar da tufa zuwa kasar Sin. Masu sayayya na kasar Sin suna bukatar ‘ya’yan itatuwa masu inganci, fiye da marasa kyau. Kasar Sin na da babbar kasuwa. Manoman kasar Afirka ta Kudu suna da ‘ya’yan itatuwa masu inganci da dandano mai dadi da kasar Sin take bukata, kuma kasar Sin na bukatar kyawawan ‘ya’yan itatuwa masu yawa.”

Kasar Afirka ta Kudu tana kudancin duniyar mu, don haka yanayin noman tufa ya bambanta da na kasar Sin, wato duk da cewa kasar Sin ba ta cikin yanayin girbin tufa, amma ana iya samun tufan da ake nomawa a kasar Afirka ta Kudu. Daga watan Janairu zuwa Mayun kowace shekara, shi ne lokacin da ake girbin tufa a Afirka ta Kudu, kuma a wannan lokacin ne ake fitar da su zuwa kasuwannin kasar Sin, sa’annan a watan Yuni, yawan tufar da aka fitar daga Afirka ta Kudu zuwa kasar Sin zai kai matsayin koli. A shekara ta 2021, yawan tufar da kasar Afirka ta Kudu ta fitar zuwa kasar Sin, ya kai ton dubu 12.3 gaba daya, adadin da ya karu da kaso 64 bisa dari. A farkon shekarar da muke ciki kuma, yawan tufar da aka fitar daga Afirka ta Kudu zuwa kasar Sin ya karu ainun.

Manajan kula da harkokin cinikayya da kasuwanni na kungiyar cinikin tufa da pear ta kasar Afirka ta Kudu, Jacques Du Preez ya bayyana cewa, a karon farko yawan tufar da Afirka ta Kudu ta fitar zuwa kasar Sin ya zarce akwatuna miliyan 1 a bana, adadin da ya karu da kaso 30 bisa dari na makamancin lokacin bara.

Jacques Du Preez ya ce:

“A al’adance, Turai ce kasuwa mafi girma da muke shigar da namu tufan da pear, amma a shekaru 10 da suka gabata, yanayin ya canza. Mu dauki tufa a matsayin misali, yanzu Afirka da Asiya su ne kasuwanni biyu mafi girma da muke kai tufan mu. A kowace shekara, mu kan fitar da kaso 30 bisa dari na yawan tufarmu zuwa Afirka, kana kaso 30 bisa dari zuwa kasashen Asiya, gaskiya su ne kasuwanni masu matukar muhimmanci a wajen mu. Tufar Afirka ta Kudu ta samu izinin shiga kasuwannin kasar Sin kusan shekaru 7 da suka gabata, da farko ba da yawa aka fitar ba, amma a bana, a karon farko adadin ya zarce akwatuna miliyan 1.”

Aikin fitar da tufa na kasar Afirka ta Kudu na da tarihin sama da shekaru 100, kuma kimanin rabin yawan tufar kasar, a kan fitar da su zuwa kasashen ketare, al’amarin da ya sa kasar take kokarin raya sana’ar fitar da tufa irin ta zamani. Jacques Du Preez ya kara da cewa, aikin fitar da amfanin gona zuwa kasashen waje, ciki har da tufa, na taka muhimmiyar rawa a fannin habaka tattalin arzikin Afirka ta Kudu, wanda kuma ya zama wani muhimmin aiki na samar da guraban ayyukan yi da ci gaban kasar.

Mista Jacques Du Preez cewa ya yi:

“Sana’ar noman ‘ya’yan itatuwa na bukatar ma’aikata masu yawa, don haka sana’ar tana da muhimmancin gaske wajen raya tattalin arziki da samar da guraban ayyukan yi a yankunan karkara. Kasar Afirka ta Kudu ta dade tana fama da matsalar rashin ayyukan yi, don haka, gwamnatin kasar ta tsara wani babban shirin raya aikin gona da sarrafa amfanin gona, inda ta ayyana aikin gona a matsayin daya daga cikin muhimman sana’o’in dake samar da guraban ayyukan yi ga al’ummar kasar. Sabili da haka, sana’ar noman ‘ya’yan itatuwa na taka muhimmiyar rawa ga ci gaban tattalin arzikin kasarmu, wadda ke iya samar da dimbin guraban ayyukan yi da kara samun kudin musanya.”

‘Yan kasuwan kasar Afirka ta Kudu suna da yakinin game da makomar kasuwannin kasar Sin, inda suke sa ran kara fitar da amfanin gonarsu masu inganci zuwa kasar Sin, da karfafa mu’amalar cinikayya tsakanin kasashen biyu. Mista Jacques Du Preez ya bayyana cewa:

“A karshen shekarar da ta gabata, Afirka ta Kudu da Sin sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fitar da pear, karon farko ke nan da za mu iya fitar da pear da muka noma zuwa kasuwannin kasar Sin. Mun shafe tsawon shekaru 15 muna kokarin cimma wannan buri, gaskiya wannan wani muhimmin al’amari ne ga sana’ar cinikin pear a Afirka ta Kudu. A bana, wasu kwantenonin pear namu sun riga sun isa kasar Sin. Yanzu muna kokarin jigilarsu, da kara sanin yadda za mu kunsa su da adana su ta yadda ba za su lalace ba. Muna sa ran a shekara mai zuwa, musamman a sabon kakar girbi, za mu iya kara fitar da pear da muka noma zuwa kasar Sin, don su ma su samu karbuwa kamar tufan mu a kasuwannin kasar.” (Murtala Zhang)