logo

HAUSA

Kasar Sin za ta ci gaba da nacewa ga manufar bude kofa yayin da take raya bangaren makamashi

2022-11-08 14:25:37 CMG Hausa

Sheng Qiuping, mataimakin ministan kasuwancin kasar Sin, ya furta a yau Talata cewa, kasar Sin za ta ci gaba da nacewa ga manufarta ta bude kofa ga kasashen ketare, yayin da take raya bangaren makamashi, kamar yadda hakan ke kushe cikin rahoton da aka gabatar a taron wakilan jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 20.

A cewar jami’in, ci gaban harkokin kasuwannin makamashi na kasar Sin, zai amfani dukkan kasashe masu samar da makamashi, da wadanda suke saye, ko kuma cinikinsa, da baiwa kasashe daban daban damammaki masu inganci na yin hadin gwiwa.

Sheng ya bayyana haka ne yayin taron cinikin danyen mai na kasar Sin karo na 11, da ya gudana duk a yau Talata.

A cewar Sheng, a gabar da duniyarmu ke fama da sauye-sauyen yanayin siyasa da yaduwar annobar COVID-19, ya zama dole kasashe daban daban su kara yin mu’amala, da sauya tsayin amfani da makamashi zuwa maras gurbata muhalli, gami da kokarin hadin gwiwa, ta yadda za a raya cinikin mai da iskar gas yadda ake bukata. (Bello Wang)