logo

HAUSA

Yin amfani da yanar gizo wajen raya duniya

2022-11-08 20:43:24 CMG Hausa

Abokaina, ko kun taba zuwa kauyen Tobolo na jihar Ogun? A can za ku iya ganin yadda yanar gizo ta Internet, da sauran fasahohin sadarwa na zamani suke haifar da sauye-sauye ga zaman rayuwar mutane.

Ko da yake babu wutar lantarki a kauyen Tobolo, amma ya samu turken sadarwar wayar salula na kansa. Mutanen kauyen suna kiran wannan turken sadarwa, da wani kamfanin Sin ya kafa shi, da taken “sanda”, saboda ba shi da girma. Amma duk da haka, na’urar na da inganci: Tana aiki ne bisa yin amfani da zafin rana, kana layin da ta samar ya shafi kauyen Tobolo da sauran kauyuka makwabtansa. Idan ana ruwan sama, ko babu rana, wannan turke na iya ci gaba da aikin har tsawon sa’o’i 48.

Kafin a samu layi, mutanen kauyen Tobolo su kan hau itace don buga waya. Saboda a can sama ana iya samun layi na kasar Benin. Sai dai kudin layin yana da tsada, kana a kan samu matsalar katsewar layin, ga kuma wahalar hawa itace.

Zuwa yanzu, mutanen kauyen suna iya yin amfani da wayar salula wajen tuntubar abokai cikin matukar sauki. Shago na chajin waya ya samu karin kasuwanci sosai, ganin yadda kashi 80% na mazauna kauyen suka fara yin amfani da wayar salula. Ban da wannan kuma, wasu sabbin kantuna sun fara aiki bi da bi a cikin kauyen, bisa yadda mutanen kauyen suke samun bayanan kasuwanci a kai a kai ta wayar salula.

Labarin kauyen Tobolo wani misali ne game da yadda kasar Sin da kasashen Afirka suke kokarin aiwatar da shawarar kafa al’umma mai makomar bai daya a fannin yanar gizo ta Internet da fasahohin sadarwa, wanda kasar Sin ta gabatar. Wadda ta shafi hadin gwiwa don gina kayayyakin more rayuwa ta fuskar aikin sadarwa, da ba da taimako ga mutane masu karamin karfi, da dai sauransu.

Sai dai me ya sa kasar Sin ta ba da shawarar kafa wata al’umma mai makomar bai daya ta bangaren yanar gizo ta Internet a duniya? Dalilin shi ne neman daidaita wasu matsalolin da ake fuskanta a yanzu, inda wasu kasashe ke son yin amfani da fifikonsu a fannin kimiyya da fasaha, wajen kokarin mai da yanar gizo ta Internet wani makami, ta yadda za su iya kiyaye matsayinsu na yin babakere a duniya. Ko da yake fasahar yanar gizo fasaha ce ta zamani, amma suna neman yin amfani da ita don aiwatar da tsohon tunani na kashin dankali.

Abun tambaya a nan shi ne, da yin amfani da fasahar yanar gizo wajen yin babakere a duniya, da kuma yin amfani da ita wajen kyautata zaman rayuwar dan Adam, wane ne ya fi dacewa? Na san amsar hakan na cikin zuciyar kowa. (Bello Wang)