logo

HAUSA

Sojojin MINUSMA dake Mali sun jikkata

2022-11-08 10:52:34 CMG HAUSA

 

Mai magana da yawun MDD Stepahanie Tremblay ta bayyana cewa, wasu sojojin dake aikin tabbatar da zaman lafiya karkashin laimar MDD (MINUSMA) guda 6 ’yan kasar Togo sun ji rauni, bayan da jerin gwanon motocin da suke ciki, ya taka wasu abubuwan fashewa da aka binne a kan hanya, kuma yanzu haka suna samun kulawar jami’an lafiya a birnin Sevare dake kasar Mali.

Staphanie ta bayyana cewa, sojojin sun samu raunuka ne, bayan da jerin gwanon motocin da suke ciki ya taka wasu abubuwan fashewa guda biyu a garin Douentza dake yankin Dangol Bore. Motoci biyu masu sulke dake cikin ayarin sojojin sun lalace, kana ragowar ayarin motocin sun isa garin Mopti ranar Lahadi da maraice ba kuma tare da wani ya samu rauni ba.

Sai dai a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na tiwita a karshen mako, shugaban tawagar dake aikin wanzar da zaman lafiya ta MDD (MINUSMA) a kasar Mali, El-Ghassim Wane, ya bayyana cewa, abubuwan da suka faru, sun nuna irin barazanar da ake fuskanta a halin yanzu, amma a cewarsa, hakan ba zai taba karya lagon kokarin tawagar ta MINUSMA, na ci gaba da kare rayukan jama’a ba. (Ibrahim Yaya)