logo

HAUSA

Hatsarin mota ya yi sanadin mutuwar mutane 3 a kudancin Nijeriya

2022-11-08 10:49:05 CMG Hausa

Mutane a kalla 3 sun mutu, yayin da wasu 3 suka jikkata, sanadiyyar hadarin mota da ya auku da sanyin safiyar jiya Litinin, a jihar Ogun dake kudu maso yammacin Nijeriya.

Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasar a jihar Ogun, Ahmed Umar, ya shaidawa manema labarai a Abeokuta babban birnin jihar cewa, wata karamar motar daukar kaya ta kubcewa direba a kan babban titin jihar saboda gudun wuce sa’a, inda motar ta hautsina tare da rutsawa da mutane.

Ya ce mutane 3 sun mutu, wasu 3 kuma sun jikkata. Yana mai cewa, mutane 6 da suka hada da maza hudu da mata 2 ne a cikin motar.

Ya kara da cewa, an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti mafi kusa, yayin da aka kai gawar mamatan zuwa dakin ajiye gawarwaki domin ‘yan uwansu su tantancesu. (Fa’iza Mustapha)