logo

HAUSA

Jakadan Sin dake Nijeriya ya gana da shugaban hukumar shige da fice ta Nijeriya

2022-11-08 14:15:13 CMG HAUSA

 

Jakadan Sin dake Nijeriya Cui Jianchun ya gana da shugaban hukumar shige da fice ta Nijeriya Idris jiya Litinin.

Yayin ganawar, jakada Cui ya bayyana cewa, ofishin jakadancin Sin dake Nijeriya ya dade yana dora muhimmanci da kuma kiyaye ’yanci da moriyar kamfanoni da Sinawa dake kasar bisa doka, yana kuma karfafawa kamfanoni da Sinawa gwiwa da jagorantansu, don su tafiyar da ayyukansu bisa dokokin kasar Nijeriya, da muntunta al’adun kasar da kuma ba da gudummawa ga al’ummomin wuraren da suke gudana da ayyukansu a Nijeriya.

Ya ce, yana fatan bangaren Nijeriya zai dora muhimmanci kan dangantakar abokantaka da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, da tabbatar da mu’amala tsakanin al’ummominsu bisa doka, da daukar managartan matakai wajen kiyaye tsaro da hakkokin jama’ar Sin dake Nijeriya.

Bangaren Sin yana son yin aiki tare da bangaren Nijeriya, wajen inganta amincewa da juna a fannin siyasa, da hadin gwiwar tattalin arziki, da tsaro, da hadin kai tsakanin kasa da kasa, da mu’ammala tsakanin jama’a, da ta al’adu tsakanin Sin da Nijeriya da kiyaye zaman lafiya tsakanin kasashen biyu tare.

A nasa bangare kuwa Idris ya bayyana cewa, ya yi farin ciki da babban sakamakon da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu ta haifar a dukkan fannoni. Babban jami’in ya ce, yana dora muhimmanci kan abin da fannonin dake shafar bangaren Sin, kana zai ci gaba da yin cudanya da ofishin jakandancin Sin dake Nijeriya, domin kara inganta tsarin tabbatar da doka da oda, da samar da sauki da daidaikun ayyuka masu inganci ga kamfanoni da al’ummar Sinawa a fannonin zuba jari da gudanar da cinikayya da karatu da kuma rayuwa a Najeriya. (Safiyah Ma)