logo

HAUSA

Ya kamata Birtaniya ta yi shawarwari kan ikon mallakar tsibiran Malvinas

2022-11-07 21:30:03 CMG Hausa

A kwanan nan ne ministan harkokin wajen kasar Birtaniya James Cleverly, ya bayyana cewa, kasarsa da kasar Mauritius, sun riga sun yanke shawarar gudanar da shawarwari kan batun da ya shafi ikon mallakar tsibiran Chagos, da sa ran cimma yarjejeniya a farkon shekara mai kamawa. An maida irin wannan ra’ayin kasar Birtaniya, a matsayin wani muhimmin matakin da aka dauka, wajen daidaita rikicin ikon mallakar tsibiran Chagos.

Tsibiran Chagos suna tsakiyar yankin ruwan tekun Indiya, yankuna ne da kasar Mauritius ta mallaka tun asali. A shekara ta 1965, a matsayin wani sharadin da aka gindayawa Mauritius don ta samu ‘yancin kai, kasar Birtaniya ta ware tsibiran Chagos daga Mauritius don su zama “yankunan dake karkashin mulkin Birtaniya a tekun Indiya”, ta kuma ce za ta mayar da su a lokacin da ya dace. Bayan da Mauritius ta samu ‘yancin kai a shekara ta 1968 har zuwa yanzu, ta dade da bukatar Birtaniya da ta maido mata da tsibiran.

Kamar batun da ya shafi tsibiran Chagos, batun tsibiran Malvinas, shi ma ya wakana ne a lokacin mulkin mallaka na kasar Birtaniya. A shekara ta 1816, kasar Argentina ta gaji ikon mallakar tsibiran Malvinas, bayan da ta samu ‘yancin kai daga mulkin mallakar kasar Sifaniya, amma Birtaniya ta dauki matakan soja, har ta kwace ikon mallakar tsibiran a shekara ta 1833. A shekara ta 1965, an zartas da kudiri mai lamba 2065 a wajen babban taron Majalisar Dinkin Duniya, inda aka bukaci kasashen Birtaniya da Argentina, da su daidaita rikici ta hanyar shawarwari. Kana kuma, har sau sama da 30, kwamitin musamman na kawar da matsalar mulkin mallaka na MDD, ya zartas da kudirori don bukatar kasar Birtaniya ta yi shawarwari da kasar Argentina. Amma Birtaniya ta yi biris da haka.

Daga cikin yankuna 17 da har yanzu suke karkashin mulkin mallaka a duniya, akwai guda 10 dake karkashin mulkin Birtaniya. Ba rikicin ikon mallakar tsibiran Chagos kawai ya kamata ta warware ba, kamata ya yi ma ta gudanar da shawarwari tun da wuri tare da Argentina kan batun tsibiran Malvinas. A wannan karnin da muke ciki, ra’ayin mulkin mallaka, da ra’ayin nuna babakere ba za su samu nasara ba. Dole ne kasar Birtaniya ta daidaita wadannan matsalolin tarihi yadda ya kamata! (Murtala Zhang)