logo

HAUSA

Yawan jarin da kasar Sin ta zuba kai tsaye a ketare ya kai matsayin gaba na uku a duniya cikin jerin shekaru goma da suka wuce

2022-11-07 16:44:57 CMG Hausa

 

A yau Litinin, ma'aikatar kasuwanci, da hukumar kididdiga, da kuma hukumar kula da musayar kudade ta kasar Sin, sun fitar da rahoto mai taken “kididdigar jarin da kasar Sin ta zuba kai tsaye a ketare na 2021”. Inda aka bayyana cewa, a shekarar 2021, yawan jarin da kasar Sin ta zuba kai tsaye a kasashen ketare ya kai dala biliyan 178.82, wanda ya karu da kashi 16.3 cikin dari bisa na shekarar 2020. Lamarin da ya sa kasar Sin ta kai matsayin gaba na uku a duniya, cikin jerin shekaru goma da suka gabata.

Ya zuwa karshen shekarar 2021, yawan kamfanonin da kasar Sin ta kafa a kasashen da shawarar "Ziri daya da hanya daya" ta shafa ya zarce dubu 11, wanda ya kai kusan rubu’i bisa na kamfanonin da Sin ta kafa a ketare. Haka kuma yawan jarin da kasar ta zuba ga kasashen kai tsaye ya kai dala biliyan 24.15, wanda ya kai matsayin koli a tarihi, wato kashi 13.5 cikin dari ne bisa na yawan jarin da kasar Sin ta zuba a ketare a duk shekara.(Safiyah Ma)