logo

HAUSA

Ma’aikatar harkokin wajen Sin ta maida martani game da sanarwar kungiyar G7 da ta shafi kasar

2022-11-07 20:18:38 CMG Hausa

Kwanan nan ne ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar G7, suka fitar da wata sanarwar hadin-gwiwa a birnin Münster na kasar Jamus, sanarwar da ta jibanci harkokin cikin gidan kasar Sin, ciki har da batutuwan da suka shafi Taiwan, da Hong Kong, da Xinjiang da kuma Tibet.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Zhao Lijian, ya bayyana a yau Litinin 7 ga wata cewa, sanarwar ta yi biris da babban matsayin kasar Sin, gami da hakikanin abubuwan dake faruwa, inda ta yi katsalandan cikin harkokin gidan kasar, da shafawa kasar bakin fenti, al’amarin da ya janyo matukar rashin jin dadi da adawa daga kasar Sin.

Zhao ya ce, kasarsa ta bukaci kungiyar kasashen G7, da ta yi fatali da ra’ayin cacar baki, da bambancin ra’ayin da take nunawa har kullum, da datakar da tsoma baki cikin harkokin gidan sauran kasashe, ko kuma maimaita karairayi, da daina rura wutar rikici tsakanin bangarori daban-daban, a wani kokari na kirkiro kyakkyawan sharadi ga hadin-gwiwar kasa da kasa. (Murtala Zhang)