logo

HAUSA

Kwalara a Malawi ta haddasa mutuwar mutane 200

2022-11-07 16:41:55 CMG Hausa

Ya zuwa ranar 5 ga watan Nuwamba, cutar kwalara ta riga ta haddasa mutuwar mutane 200 a kasar Malawi. Tun bayan gano mutumin farko da ya kamu da cutar a watan Maris a yankin bakin iyaka da ke kudu maso gabashin kasar har zuwa yanzu, jimillar wadanda suka kamu da cutar a kasar ta kai 6720 gaba daya, wadanda suka shafar wurare 28.

Bisa labarin da ma’aikatar kiwon lafiya ta Malawi ta bayar, an ce, karancin abinci da ruwan sha mai tsafta, babu isasshen ban daki, da kasa amfani da su yadda ya kamata, muhimman dalilai ne da suka haifar da barkewar kwalara a tsakanin al’ummomin wurin.(Safiyah Ma)