logo

HAUSA

Duniya Za Ta Dandana Kudar Matakin Da Amurka Ta Dauka

2022-11-07 14:16:04 CMG HAUSA


Daga MINA

Ran 3 ga watan nan, babban bankin Amurka ya sake sanar da kara kudin ruwa da kashi 0.75%, da nufin sassauta hauhawar farashin kayayyaki a cikin gia. Yau “duniya a zanen MINA” zai bayyana muku illar da wannan mataki zai haifar.

Wannan shi ne karo na 6 da babban bankin Amurka ya kara kudin ruwa tun farkon bana, matakin da ya sa kudin ruwan ya kai matsayin koli tun watan Jarairu na shekarar 2008. Sai dai ba a kai ga daidaita matsalar hauhawar farashin kaya ba, a maimakon haka, matakin ya kara haifar da koma bayan tattalin arzikin duniya. Bankin duniya ya ba da rahoto cewa, yawancin manyan bankunan kasa da kasa sun kara kudin ruwa a kasashensu da ba a taba ganin irinsa ba a cikin shekaru 50 da suka gabata sakamakon matakin da Amurka ta dauka. Abin da ya haifar da mummunan tasiri ga kasashe masu tasowa wadanda ke matukar bukatar ci gaba.

Kwanan baya, an saurari ra’ayin masana tattalin arziki 100 a duniya, inda suke ganin cewa, kudin ruwan da Amurka ta kara a jere, ya haifar da koman baya a duniya baki daya, kuma 90% na masanan da aka tattauna da su, sun yi hasashen cewa, saboda da mataki na Amurka, ana fuskantar karin kalubalen hauhawar farashi.

Amurka ta samar da karin kudaden dala da nufin sassauta matsalar da ta fuskanta da sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki a cikin gida, amma hakan bai kai ta ga samun nasara ba. A maimakon haka ma, sai matakin ya haifar da hauhawar farashin kayayyaki da kara gibi tsakanin mawadata da talakawa. Ba yadda zai yi sai babban bankin Amurka ya kara kudin ruwa, idan ba haka ba, jama’a za su nuna adawa da gwamnati, da haddasa rashin tabbas a zamantakewar al’umma, kana rikici da koma baya a cikin gida zai tsananta matuka. Amma, matakin da Amurka ke dauka ya shafi wasu kasashe marasa karfi, wadanda farfadowar tattalin arzikinsu ke da rauni, baya ga haddasa hasara da mummunan sakamakon da zai biyo ga irin wadannan kasashe.

 ‘Yan siyasar Amurka ba su yi la’akari da muradun jama’a da rikicin da sauran kasashe za su fuskanta ba, abin da ya dame su shi ne moriyar siyasa da ta sanya gaba. Kuma suna sane da cewa, duniya za ta dandana kudar matakan da suka dauka, kamar wannan karo da ta kara kudin ruwa. (Mai zane da rubuta:MINA)