logo

HAUSA

Zhao Lijian: Taken baje kolin CIIE na bana shi ne kara bude kofa ga waje

2022-11-07 21:40:04 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce taken baje kolin kasa da kasa na hajojin da ake shigowa da su kasar Sin ko CIIE karo na 5, wanda aka bude a ranar Juma’a 4 ga watan nan, shi ne kara bude kofa ga kasashen waje.

Zhao Lijian, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a yau Litinin, ya ce baje kolin na CIIE na bana, shi ne muhimmin bikin baje hajoji da kasar Sin ta gudanar, tun bayan kammalar taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20 a kwanakin baya, kuma bikin CIIE na bana ya ja hankalin dukkanin sassa masu ruwa da tsaki.

Jami’in ya kara da cewa, Sin za ta ingiza burin dukkanin kasashen duniya na cin gajiya daga damammakin babbar kasuwar kasar Sin, da moriyar dake tattare da kara bude kofar kasar, da ta zurfafa hadin gwiwar sassan kasa da kasa.   (Saminu Alhassan)