logo

HAUSA

Adadin wadanda suka mutu sanadiyyar hatsarin jirgin saman Tanzania a tabkin Victoria ya karu zuwa 19

2022-11-07 10:08:00 CMG Hausa

Adadin mutanen da suka mutu sanadiyyar faduwar jirgin saman kasar Tanzania, ya karu daga mutum 3 da safiyar jiya, zuwa 19 da yammacin jiya Lahadi.

Firaministan kasar Kassim Majaliwa, wanda ya ziyarci wajen da hadarin ya auku a gabar tabkin Victoria dake gundumar Bukoba na yankin Kagera da yammacin jiya Lahadi, ya ce akwai yiwuwar wasu fasinjoji sun makale cikin jirgin da ya lalace.

Hukumar kula da sufurin jiragen saman fasinja ta kasar TCAA, ta bayyana tun da farko cewa, jirgin na kamfanin Precision mai lamba 5H-PWF, ya tashi ne daga Dar es Salaam zuwa Bukoba, inda ya gamu da hadarin yayin da yake sauka, da misalin karfe 8:45 na safiya, agogon kasar.

Sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce jirgin ya fada cikin ruwa, mita 500 daga titin tashi da saukar jirage.

Ta kara da cewa, aikin ceto na gudana, kuma hukumar ta TCAA za ta sanar da al’umma yanayin da ake ciki. (Fa’iza Mustapha)