logo

HAUSA

Mene ne illolin ciwon sukari? Ta yaya za a yi rigakafi da shawo kan ciwon?

2022-11-07 11:25:24 CMG Hausa

 

Ranar 14 ga watan Nuwamba, rana ce ta ciwon sukari ta MDD. A shekarun baya-bayan nan, yawan masu kamuwa da ciwon sukari yana ta karuwa, kana karin matasa sun kamu da cutar, lamarin da ya jawo hankali sosai. MDD ta sha yin kira ga gwamnatocin kasashe da su bada muhimmanci kan kyautata kulawa da masu fama da ciwon sukari, a kokarin hana tsanantar ciwon da kuma kare su daga kamuwa da cututtukan da sukan biyo bayan kamuwa da ciwon sukari.

Alkaluman da hadaddiyar kungiyar kula da ciwon sukari ta kasa da kasa ta kaddamar sun shaida cewa, yanzu baligai kimanin miliyan 537 suna fama da ciwon sukari a duk fadin duniya, kwatankwacin baligi daya cikin ko wanne baligai 10. Ban da haka kuma, baligai miliyan 541 suna fama da matsalar sarrafa yawan sukari a jininsu a duniya, lamarin da ya nuna cewa, suna fuskantar babbar barazanar kamuwa da ciwon sukari mai nau’in 2.

Ciwon sukari, wani nau’in ciwo ne da ya dade yana addabar mutane. Masu kamuwa da ciwon su kan yi fama da matsalar karancin sinadarin insulin saboda saifarsu ba sa aiki yadda ya kamata, ko kuma jikinsu ba sa amfani da sinadarin insulin yadda ya kamata, ta haka yawan sukarin da ke cikin jininsu ya karu. A kwana a tashi, ciwon sukari zai illata zuciya, magudanar jiki, idanu, koda da jijiyoyi, kana kuma ya kan haifar da makanta, lalacewar koda, ciwon zuciya, shan inna da yanke kafaffu.

Akwai ciwon sukari masu nau’o’i guda 2. Masu fama da ciwon sukari mai nau’in 1 ba sa iya samar da sinadarin insulin da kansu, suna bukatar a yi musu allurar sinadarin don ci gaba da rayuwa. Masu fama da ciwon sukari mai nau’in 2 kuma, ba sa iya amfani da sinadarin insulin yadda ya kamata, yawansu ya kai kaso 90 cikin jimillar yawan masu fama da ciwon sukari.   

Kamuwa da ciwon sukari mai nau’in 1, ikon Allah ne, wanda ba a iya yin rigakafi. Matsalar kiba da karancin motsa jiki suna haddasa kamuwa da ciwon sukari mai nau’in 2. Hakikanin abubuwa sun shaida cewa, dan sauya salon rayuwa yana iya kare ko kuma dakatar da kamuwa da ciwon sukari mai nau’in 2, alal misali, tabbatar da daidaiton nauyin jiki, rika motsa jiki, cin abinci yadda ya kamata da daina shan taba.

Madam Zhang Chuji, likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta bayyana mana cewa, yanzu ana fadada nazarin magunguna da hanyoyin shawo kan ciwon sukari. Amma ya zuwa yanzu sinadarin insulin magani ne mafi amfani wajen shawo kan ciwon.

An gano cewa, ciwon sukari yana kara barazanar mutuwar masu fama da cutar COVID-19. Masana ilmin likitanci sun yi kira da a bada muhimmanci ga kulawa da masu fama da ciwon sukari ta hanyoyi 5, wato cin abubuwa masu gina jiki ta hanyar kimiyya, motsa jiki ta hanyar da ta dace, shan magani, sa ido kan yawan sukarin da ke jini da ilmantar da jama’a kan kiwon lafiya. (Tasallah Yuan)